Yadda aka kashe Sadiya da diyarta mai shekaru 4 a Kebbi sannan aka yanke wasu sassa na jikinsu

Yadda aka kashe Sadiya da diyarta mai shekaru 4 a Kebbi sannan aka yanke wasu sassa na jikinsu

  • Wasu marasa imani da ba a san ko su waye ba sun bi har gida sun halaka wata mata da diyarta mai shekaru hudu a garin Birnin Kebbi, jihar Kebbi
  • Bayan sun kashe Sadiya da diyarta Khadija, sai suka yanke wasu sassa na jikinsu wanda hakan yasa ake tunanin asiri za a yi da su
  • Rundunar yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da faruwa al'amarin, ta kuma ce a yanzu haka tana kan gudanar da bincike a kan kisan

Kebbi - Rundunar yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da kisan wata mata da diyarta mai shekaru hudu a gidansu da ke Birnin Kebbi, babbar birnin jihar a ranar Talata, 12 ga watan Afrilu.

Premium Times ta rahoto cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun kashe Sadiya Idris mai shekaru 25 da diyarta Khadija a daren ranar Lahadi a gidanta da ke yankin Labana Rice Mills a titin Sani Abacha, Birnin Kebbi.

Kara karanta wannan

Bayan harin Filato, yan bindiga sun sake kashe mutum 19 a wata jihar arewa

Yadda aka kashe Sadiya da diyarta mai shekaru 4 a Kebbi sannan aka yanke wasu sassa na jikinsu
Yadda aka kashe Sadiya da diyarta mai shekaru 4 a Kebbi sannan aka yanke wasu sassa na jikinsu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Yan sandan sun bayyana cewa ba a ga wasu sassa na jikin uwar da diyartata ba. An tsinci gawar tasu ne a safiyar Litinin.

Rundunar yan sandan ta kuma ce ana nan ana gudanar da bincike a kan al’amarin.

A halin da ake ciki, gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu, ya ziyarci iyalan mamatan domin yi masu ta’aziyya. Tuni aka binne uwar da diyar daidai da koyarwar addinin Musulunci.

Sai dai kuma, yayar marigayiya Sadiya, Hajiya Sahura Mukhtar ta bayyana cewa mijin marigayiyar wanda ya kasance tela ne ya bar gidansa da misalin karfe 1:00 na tsakar dare zuwa shagonsa sannan aka kashe matar tasa da misalin karfe 4:00 na asuba, rahoton Vanguard.

Ta kara da cewar, marigayiyar wacce ke shayarwa ta kuma bar yar wata uku, ta kuma bayyana ta a matsayin mace mai shiru-shiru da dauriya wacce da wuya ta sanar da yan uwanta halin da gidanta yake ciki.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe

A halin da ake ciki, mijin marigayiyar Hakilu Muhammad yana kwance a asibiti sakamakon yanke jiki da ya yi ya fadi bayan samun labarin kisan mata da diyarsa.

Yayin da ake zaton an aikata kisan ne domin yin asiri, Kebbi na daya daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren yan bindiga da ke kai farmakinsu a matsayin yan fashin daji.

Zamfara: 'Yan bindiga sun sace dalibai 5 na kwalejin lafiya da ke Tsafe

A wani labari na daban, 'Yan bindiga sun kutsa wani yanki na garin Tsafe kuma sun sace dalibai biyar na kwalejin kiwon lafiya da fasaha da ke tsafe a jihar Zamfara.

Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, lamarin ya faru ne a sa'o'in farko na ranar Laraba. Wata majiya ta sanar da cewa miyagun 'yan bindiga dauke da miyagun makamai ne suka dire gidan daliban wanda yake wajen makaranta.

Ya ce 'yan bindiga ba za su taba samun damar shiga makarantar ba saboda jami'an tsaron da ke kofar shiga.

Kara karanta wannan

An kashe mutane masu yawan gaske yayin da yan bindiga suka farmaki kauyukan Filato 4

Asali: Legit.ng

Online view pixel