Yadda na zama mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya bada labari mai taba zuciya a bidiyo

Yadda na zama mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya bada labari mai taba zuciya a bidiyo

  • Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasa ya sanar da yadda ya zama dan takara a 2014 kuma ya haye kujear mafi daraja ta 2 a kasar nan
  • Ya ce duk da ya yi kwamishina a jihar Legas, amma kwamishinoni suna da yawa don haka ko zaben karamar hukuma a lokacin ba zai iya ci ba
  • Ya alakanta nasarar da ya samu a rayuwa da yin Ubangiji, wanda shi kadai ya dafa masa har ya kai matsayin da ya ke a halin yanzu

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a watan Disamban 2021 ya yi magana kan yadda ya zama mataimakin shugaban kasa a APC a 2015.

Bidiyon da ya saki ya bayyana a watan Janairu a Twitter yayin da ake ta rade-radin cewa Osinbajo na son gaje kujerar Ubangidansa Buhari a 2023, faston kuma farfesan shari'ar ya alakanta zamansa mataimakin shugaban kasa da ikon Allah.

Kara karanta wannan

Manyan jihohin kudu maso yamma 3 da Osinbajo zai iya rasawa idan ya zama dan takarar APC

Yadda na zama mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya bada labari mai taba zuciya a bidiyo
Yadda na zama mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya bada labari mai taba zuciya a bidiyo. Hoto daga Yemi Osinbajo
Asali: Facebook

Binciken da Legit.ng ta yi ya nuna cewa mataimakin shugaban kasa ya yi magana kan matsayinsa ne yayin da ya ziyarci Rabaren Udochi M Odikanwa a taron gangamin Restoration Life Assembly International da aka yi a watan Disamban 2021.

Mataimakin shugaban kasan, fasto kuma farfesan shari'ar ya alakanta matsayinsa da ikon Ubangiji inda yace ba shi da ko karfin cin zaben shugaban karamar hukuma a lokacin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Ku duba, babu me samun komai ba tare da Ubangiji ya bashi ba. Ya ce shi ke bada dukkan kyauta. Kowacce kyautar arziki daga wurinsa take zuwa. Gumurzun bai yi sauri ba kuma yakin bai yi kamari ba.
"Lokaci da dama kowa na iya samu. Ubangiji kenan. Saboda haka ne yau na zama mataimakin shugaban kasa. Babu yadda za a yi in iya cin zaben shugaban karamar hukuma a 2014, babu. Babu Wanda ya sanni. Tabbas na yi kwamishina a Legas amma akwai tarin kwamishinoni.

Kara karanta wannan

2023: Amaechi ya fara neman shawarwari, ya ziyarci sarakunan Daura, Kano da Bichi

"Babu Wanda ya sanni amma Ubangiji ya dafa min. Ya saka min hannu, dare daya aka zabe ni. Ina jiran in tafi kotu, ina zaune da abokan aikina muna shirin zuwa kotun koli washegari."

Ya kara da cewa:

"Karfe 1 na dare aka kira ni. "Ka na ina? Ga mu nan za mu daukeka. Nace me kuke nufi da daukata? Ina shirin zuwa kotun ne gobe da safe. A nan aka sanar da cewa an zabi in zama dan takarar mataimakin shugaban kasar jam'iyyata. Na san yin Ubangiji ne, bani da ko shakka a zuciyata.
"Dalilin kuwa da Ubangiji yasa na kai wannan matsayin a wannan lokacin, shi kadai ya sani."

Shugaban kasa: Yadda Farfesa Yemi Osinbajo zai ayyana shirin gaje kujerar Buhari a yau

A wani labari na daban, rahotanni na nuna cewa Farfesa Yemi Osinbajo zai sanar da Duniya niyyarsa na tsayawa takarar shugaban kasa a yau Litinin, 11 ga watan Afrilu 2022.

Kara karanta wannan

Zan daura daga inda Buhari ya tsaya: Alkawura 10 na Osinbajo idan ya zama shugaba a 2023

Jaridar Premium Times ta kawo rahoto da ya tabbatar da cewa Mai girma mataimakin shugaban kasa zai nemi ya gwabza da tsohon mai gidansa, Bola Tinubu.

Tun ba yau Farfesa Yemi Osinbajo ya fara wannan shirye-shirye ba, amma sai a karshen makon da ya gabata zuwa yanzu ne abubuwa suke kara bayyana a fili.

Asali: Legit.ng

Online view pixel