Ya muka kare da Buhari balle Osinbajo: Tsokacin lauya ga takarar Osinbajo a 2023

Ya muka kare da Buhari balle Osinbajo: Tsokacin lauya ga takarar Osinbajo a 2023

  • An bukaci mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya manta da kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa domin amfanin ‘yan Najeriya
  • A cewar Festus Ogun, ya kamata mataimakin shugaban kasar ya nemi gafarar ‘yan Najeriya kan wahalhalun da gwamnatin APC ta kawo wa Najeriya
  • Ya ci gaba da cewa, a karkashin su Osinbajo, tattalin arzikin kasar nan ya durkushe, a sakamakon haka bai kamata a kara amincewa da irinsu ba

Festus Ogun, daya daga cikin lauyoyin Najeriya masu tasowa kuma mai fafutukar kare hakkin bil adama, ya yi kira ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da ya manta da batun tsayawa takarar shugabancin kasar nan domin amfanin kasar.

A cewar Ogun, wanda ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da Osinbajo, mataimakin shugaban kasar ya kasance jigo a gwamnatin Buhari, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zan daura daga inda Buhari ya tsaya: Alkawura 10 na Osinbajo idan ya zama shugaba a 2023

Martanin wani lauya kan kudurin Osinbajo na gaje Buhari
Ya muka kare da Buhari balle Osinbajo: Shaguben lauya ga takarar Osinbajo ta 2023 | Hoto: ProfOsinbajo
Asali: Facebook

Ya kara da cewa gwamnatin su Osinbajo ta kawo wa Najeriya wahalhalun da ba a taba gani ba, wadanda suka durkusar da kasar a zahiri.

Musamman ma ya yi kira ga mataimakin shugaban kasar da ya nemi gafarar 'yan Najeriya kan halin kuncin da gwamnatin su ta jawo wa Najeriya maimakon tsayawa takarar shugaban kasa.

A cewarsa:

"Alherin ‘yan Najeriya a ce Osinbajo bai tsaya tsaya Shugaban kasa ba. A shekarar 2015 ya fito takara a jam’iyyar APC tare da Janar Buhari wanda ya durkusar da kasarmu gaba daya. Ba za ku iya raba Osinbajo da gazawar Buhari ba. Ya kamata ya nemi gafara, ba takara ba.
"Tare suka kawo wa ‘yan Najeriya wahala da yunwa da radadi da mutuwa a cikin shekaru 7 da suka gabata da sunan kawo sauyi.

Kara karanta wannan

Ba na shakkan Tinubu ko Osinbajo, duk zan kada su - Yahaya Bello

"Osinbajo yana aiki ne a tsarin mulkin da ke alfahari da rashin mutunta doka da tsarin mulkin dimokuradiyya. Tunanin takara kadai cin mutunci ne."

Hakazalika, ya yi tsokaci da cewa, kasancewar Osinbajo masanin doka, duk da haka aka hada kai dashi wajen bata romon dimokradiyya a Najeriya a mulkin Buhari.

Abin da ‘Yan Facebook da Twitter ke ta fada kan shirin takarar Osinbajo a zabe mai zuwa

A wani labarin, a wannan rahoto, mun tattaro abin da jama’a ke fada a dandalin sada zumunta a kan takarar mai girma mataimakin shugaban na Najeriya.

Ga na mu nan. Mu na nan! Shugaban kasar gobe. @ProfOsinbajo #Starboy #OsinbajoDeclares.

Haka dai 'yan Najeriya da dama suka dinga nuna ra'ayoyinsu ga fatan Osinbajo na gaje Buhari a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel