Manyan jihohin kudu maso yamma 3 da Osinbajo zai iya rasawa idan ya zama dan takarar APC

Manyan jihohin kudu maso yamma 3 da Osinbajo zai iya rasawa idan ya zama dan takarar APC

Cece-kuce ya biyo bayan ayyana kudirin son gaje Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi.

Hakan ya nuna za a kai ruwa rana a yayin zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a inda za ta zabi dan takararta na shugaban kasa.

Ayyana neman takarar Osinbajo na nufin sa kafar wando daya da tsohon ubangidansa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda ya kwallafa rai a kan son zama shugaban kasar Najeriya.

Manyan jihohin kudu maso yamma 3 da Osinbajo zai iya rasawa idan ya zama dan takarar APC
Manyan jihohin kudu maso yamma 3 da Osinbajo zai iya rasawa idan ya zama dan takarar APC Hoto: Yemi Osinbajo
Asali: Facebook

Mataimakin shugaban kasar wanda ya hau karagar mulki ta sanadiyar huldarsa da Tinubu bashi da wani kafaffen tsari na siyasa.

Ana kallon Tinubu a matsayin babban gayya a siyasar kudu maso yamma inda daga nan ne Osinbajo ya fito.

Kara karanta wannan

Zan daura daga inda Buhari ya tsaya: Alkawura 10 na Osinbajo idan ya zama shugaba a 2023

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wannan rahoto, Legit Hausa ta duba wasu manyan jihohi da Osinabjo ka iya rasawa idan ya zama dan takarar jam’iyya mai mulki a zaben 2023 sannan Tinubu zai janye ragamar siyasarsa daga APC.

Jihohin da Osinbajo zai iya rasawa a kudu maso yamma

1. Jihar Ondo

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya kasance dan kashenin babban jagoran na APC na kasa. Baya ga haka Akeredolu na da karfi a jihar wanda hakan zai sa ya yi matukar wahala wani daban ya zo sannan ya lashe zabe a jihar. Ana kallonsa a matsayin mutum mai matukar biyayya ga wadanda yake goyon baya.

Saboda haka, zai yi wuya mataimakin shugaban kasa ya kawo jihar Ondo idan ya zama dan takarar shugaban kasa na APC – idan Tinubu ya sauya sheka zuwa wata jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa: Yadda Farfesa Yemi Osinbajo zai ayyana shirin gaje kujerar Buhari a yau

2. Jihar Lagas

Tsohon gwamnan jihar Lagas kuma mai neman takarar shugaban kasa, Tinubu na da karfi sosai a jiharsa. A yanzu haka, gaba daya tsarin siyasar jihar a hannun Tinubu take. Babu makawa cewa Osinbajo zai sha kaye a wannan jihar.

A matsayinsa na mataimakin shugaban kasa, Osinbajo bai da wani kafaffen tsari a Lagas kuma a matsayin dan takara, babu yadda hakan zai sauya kasancewar Tinubu na da karfi a siyasar jihar.

3. Jihar Osun

A bayyane yake cewa Tinubu dan jihar Osun ne. baya ga haka, ya taka rawar gani wajen wanzuwar gwamna mai ci a jihar wanda yake dan uwansa ne na jini.

Osun ta kasance jiha da mataimakin shugaban kasar ba zai kai labari ba a zaben shugaban kasa na 2023.

APC ta soki Osinbajo don zai yi takara da Tinubu, ta ce bai tsinana komai ba a shekara 7

A wani labarin, mai magana da yawun jam’iyyar All Progressives Congress, APC a jihar Legas, Seye Oladejo, ya soki mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

Kara karanta wannan

Ziyarar Kaduna: Tinubu ya samu tabarraki daga wajen Sheikh Dahiru Bauchi

Jaridar Premium Times ta ce Seye Oladejo ya caccaki Farfesa Yemi Osinbajo ne saboda ya ayyana niyyar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 a karkashin APC.

Kakakin jam’iyyar ta APC na reshen jihar Legas ya ce sun san da take-taken Osinbajo, abin da su ke bukata shi ne ‘yan siyasa su hadu a wajen zaben tsaida gwani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel