Babu hankali a lamarin: Martanin Shehu Sani da wasu 'yan Najeriya kan dakatar da Sheikh Nuru Khalid

Babu hankali a lamarin: Martanin Shehu Sani da wasu 'yan Najeriya kan dakatar da Sheikh Nuru Khalid

  • An dakatar da Sheikh Nuru Khalid a matsayin babban limamin masallacin Juma’a na Apo da ke Abuja bisa wa’azin da ya yi a kan gwamnati mai ci
  • Hudubar Juma’ar da ta gabata da ya yi ta yi martani ne ga harin jirgin kasan Kaduna, wanda nan take kwamitin gudanarwa na masallacin ya dakatar da shi
  • ‘Yan Najeriya irinsu Sanata Shehu Sani sun yi caccaka a kan wannan mataki inda suka yaba da jajircewar Limamin na fadin gaskiya a kan masu mulki

An caccaki kwamitin masallacin Abuja bayan dakatar da limamin masallacin Juma'a na Apo Sheikh Nuru Khalid sakamakon caccakar bangarori daban-daban na gwamnati.

Daya daga cikin wadanda suka yi Allah-wadai da matakin dakatar da malamin dai shi ne tsohon dan majalisar dattawa daga Kaduna ta tsakiya kuma mai fafutukar siyasa da zamantakewa, Shehu Sani.

Kara karanta wannan

Cikakkiyar hudubar Juma’ar da ta jawo aka dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limanci a Apo

Martanin 'yan Najeriya game da dakatar da Nuru Khalid
Babu hankali a lamarin: Martanin Shehu Sani da 'yan Najeriya kan dakatar da Imam Nuru Khalid | Hoto: newsdigest,ng
Asali: UGC

Sani ya bi sahun ‘yan Najeriya da dama don bayyana ra’ayinsa a shafin Twitter. Ya bayyana dakatarwar a matsayin rashin hankali tsagwaronsa.

Rubutunsa na Twitter ya ce:

“Dakatar da limamin masallacin juma’a na Apo Sheikh Nuru Khalid da kwamitin kula da masallacin suka yi, bai dace ba. Sukar da ya yi wa gwamnati ya nuna ra’ayin yawancin ‘yan Najeriya, ya fadi gaskiya a kan mulki a daidai lokacin da ya dace. Ina kira ga kwamitin da ya sake shawara."

Dan siyasar ya kara da cewa yayin da sauran malaman addinin Islama ke kame baki yayin da shugabannin Najeriya ke ci gaba da yin biris da halin da al'umma ke ciki, Sheikh Khalid da wasu tsirarun mutane sun tashi tsaye domin kira ga kawo gyara.

Me yasa aka dakatar da Sheikh Nuru Khalid?

Kara karanta wannan

Dakatar da Sheikh Nuru Khalid: Kungiyoyi sun yi martani masu zafi

A wata huduba a ranar Juma’a, 1 ga watan Afrilu, Sheikh Khalid ya caccaki gwamnati mai ci a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan tabarbarewar tsaro a kasar.

Ya kuma shawarci masu kada kuri'u a kasar kan su ba 'yan siyasa sharadi gabanin zabe, idan suka gaza cikawa su ki fitowa zabe. Kwana daya bayan hudubarsa, kwamitin masallacin rukunin gidajen 'yan majalisu da ke Apo a Abuja, ya dakatar da malamin.

Shugaban kwamitin, Sanata Saidu Muhammed Dansadau, ya ce an dakatar da limamin ne saboda wa’azin da ya yi wanda yace ka iya tada hankalin jama’a.

Wasu 'yan Najeriya sun yi Allah-wadai da dakatarwar da aka yi wa Sheikh Khalid

Gimba Kakanda @gimbakakanda ya rubuta a Twitter:

“Yanzu na karanta cewa an dakatar da Sheikh Nuru Khalid na Masallacin Juma’a na Apo saboda sukar Buhari na kin zuwa Kaduna kan harin jirgin kasa na ranar Litinin da ta gabata. Muna zargin Malaman mu da kasancewa masu ba da damar yin mummunan shugabanci, a nan kuma mun samu wanda aka tsangwama don fadin gaskiya."

Kara karanta wannan

Yan Kwamitin Masallaci sun dakatad da Sheikh Nuru Khalid daga Limanci a Abuja

Shazy @ShehuZubair ya lura cewa malamin ya yi abin da ya dace anan duniya. Ya ce za su iya samun nasarar dakatar da shi a nan duniya ne kawai.

FS Yusuf @FS_Yusuf_ ya bayyana cewa:

"Zan yi alfahari da Sheikh Nuru Khalid har abada, yana da matukar karfin hali wajen fadin gaskiya da sanin cewa za ta iya jawo abubuwa da yawa, maslahar da muka ki yarda da ita a yau, ita ce za ta sanya wani tsari na gobe ga wasu. Da haka zamu gina duniya mai adalci."

Cikakkiyar hudubar Juma’ar da ta jawo aka dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limanci a Apo

A rahotonmu na baya, Legit.ng Hausa ta saurari wannan huduba ta Sheikh Nuru Khalid, ta fassara ta zuwa harshen Hausa. The Cable ta kawo asalin hudubar cikin harshen Ingilishi.

“Shin babu wanda zai dauki laifi ne? Ina ganin cewa dukkaninmu mun gaza. Ma’ana – Na gaza a matsayin Limami, na gagara fahimtar da ku cewa rai na da daraja.”

Kara karanta wannan

Ana maganar rufe Majalisa domin tursasa Shugaban kasa ya tashi-tsaye kan lamarin tsaro

“Dukkanku kun gaza a matsayinku na iyaye wajen nunawa ‘ya ‘yanku cewa kashe-kashe ba abu mai kyau ba ne. Shugabanni, ‘yan siyasa, da gwamnoni sun gaza.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel