Nasara daga Allah: Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram/ISWAP da yawa, sun ceto mutane

Nasara daga Allah: Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram/ISWAP da yawa, sun ceto mutane

  • Sojojin haɗin guiwa sun samu nasarar halaka mayaƙan kungiyar ta'addancin Boko Haram da ISWAP da dama a Tafkin Chadi
  • Wata majiya ta bayyana cewa yan ta'addan sun kwashi kashin su a hannun sojojin a wasu artabu biyu da suka fafata
  • Wani mai sharhi kan harkokin tsaro ya ce sojoji sun ceto mata 21 da kuma kananan yara 11 daga hannun yan ta'adda

Dakarun sojojin haɗin guiwa na ƙasashe (MNJTF) sun sheƙe yan ta'addan kungiyar Boko Haram/ISWAP da dama a kokarin tsaftace yankin Tafkin Cadi daga ta'addanci.

Operation Lake Sanity da dakarun sojin ke cigaba da matsa ƙaimi a kai na cigaba da haifar da ɗa mai ido a yankin, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Dakarun Soji sun samu nasara kan Boko Haram.
Nasara daga Allah: Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram/ISWAP da yawa, sun ceto mutane Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Fitaccen mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ranar Alhamis, ya bayyana cewa Sojojin sun ceto mata 21, da kanana yara maza 11 daga ranar 28 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jirgin yaƙin Sojojin Najeriya ya halaka dandazon yan bindiga a bodar Kaduna da Neja

Wata majiya da ta nemi a ɓoye bayananta ta ce gwarazan Sojojin sun samu nasarar share Cemente, Bagadaza, Zanari da Wulgo duk a ƙaramar hukumar Gamborun Ngala, jihar Borno.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ce:

"An yi artabu sau biyu da mayakan kungiyar Boko Haram da ISWAP a Zinari da kuma yankin tashar jirgin ruwa kuma dukkan hare-haren biyu Sojoji sun dakile su."

A cewar majiyar, mafi yawan yan ta'adda sun tsere da munanan raunukan harbin bindiga a dukkan waɗan nan Artabu guda biyu da suka fafata da Sojoji.

Yankin tafkin Chadi na ɗaya daga cikin wuraren da yan Boko Haram suka addaba a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

A wani labarin kuma An sake gano wani Bam da aka ɗana a Kaduna, awanni bayan warware wani

Mutane sun sake gano wani abun fashewa a yankin Shanono dake Anguwar Rigasa karamar hukumar Igabi ta Kaduna.

Kara karanta wannan

Yadda Jami’an tsaro suka yi burus duk da an samu rahoton za a kai wa jirgin kasa hari

Wani mazaunin yankin ya ce kananan yara ne suka fara gano Bam ɗin a cikin Jarka a wurin da aka ga na jiya Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel