Hoton kyakyawan rubutun shugaba Buhari da ya bayyana ya kayatar da mutane

Hoton kyakyawan rubutun shugaba Buhari da ya bayyana ya kayatar da mutane

  • Kyakyawan rubutun shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wanda yayi a jihar Legas a kamfanin Dangote
  • A ranar Talata shugaban kasan ya kaddamar da kamfanin taki na Dangote inda ya dauka alkalami da takarda ya rubuta sakon taya murna da kansa
  • A cikin sakon, ya sanar da cewa kafa kamfanin yana da cikin kokarin gwamnatinsa na taimakawa manoma da yan Najeriya wurin inganta rayuwa

Joe Igbkwe, hadimin Gwamna Babajida Sanwo-Olu, a ranar 22 ga watan Maris, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rubuta sako da rubutunsa a Ijebu Lekki da ke Legas, inda ya kaddamar da kamfanin taki na Dangote.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi rubutun ne yayin da ya tsinke shingen shiga kamfanin, alamun kaddamar da aikin da ya lamushe biliyoyi wanda babu shakka zai habaka tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kudin Dangote sun kara yawa da N1.5bn yayin da aka kaddamar da kamfanin takinsa

Hoton kyakyawan rubutun shugaba Buhari da ya bayyana ya kayatar da mutane
Hoton kyakyawan rubutun shugaba Buhari da ya bayyana ya kayatar da mutane. Hoto daga Joe Igbkwe
Asali: Facebook

A sakon, Buhari ya ce wannan aikin babu shakka ya yi daidai da kudirin gwamnatinsa na inganta rayuwar 'yan Najeriya, ballantana manoma.

Ya kara da cewa, kaddamar da kamfanin na nuna cigaban da za a samu a bangaren dogaro da kai na 'yan Najeriya.

Takaitaccen sakon da ya rubuta amma cikin rubutunsa mai matukar kyau yace:

"Kamfanin takin Dangote da yanzu na kaddamar ya yi daidai da kokarin gwamnatinmu na sauya rayuwar manoma tare da kara musu kudin shiga da kuma ceto karfin kasar nan a fannin canji na kasashen ketare.
"Wannan taro a Ibeju Lekki a yau alama ce na cewa babu abinda ya gagari Najeriya in har akwai 'yan kasuwa masu hangen nesa irinsu Aliko Dangote.
"Ina taya murna."

'Yan Najeriya sun yi martani

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira jihar Legas kaddamar da ayyuka

Tuni 'yan Najeriya suka garzaya shafin Facebook din Joe suka fara martani.

Amma wasu mutane sun dinga bayyana cewa shugaban kasar mutum ne mai nagarta kuma hakan yasa ba zai iya karya da kyakyawan rubutunsa ba.

Ga wasu daga cikin martanin:

Amb Kuseme: "Idan zai iya wannan kyakyawan rubutun, me yasa kasar nan take a haka? Akwai wani abu da bamu sani bane? Tambayar 'yan uwana nake yi da ke kasar Igbo."

Arome Attah:

"Babu wuta, babu mai kuma rayuwa ta yi tsanani, wa kyan rubutun zai taimaka?"

Samuel Omoloa Edema:

"Hmmm. A tunanina zai ce babu abinda zai gagaremu da shugabanni masu hangen nesa, amma sai cewa yayi babu abinda zai gagara da 'yan kasuwa masu hangen nesa... Hakan da kyau."

Ralph O. Ahanonu:

"Samuel Omoloa Edema, Dangote shugaba ne mai hangen nesa kuma dan kasuwan Najeriya mai hangen nesa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel