An gurfanar da matar da ta raba man fetur a wajen Biki a Legas

An gurfanar da matar da ta raba man fetur a wajen Biki a Legas

  • Mai bukin murnar bata sarauta da tayi rabon galolin man fetur ga wadanda suka halarci bikin ta shiga komar hukuma
  • Erelu Okin ta bayyana cewa ta raba fetur ne saboda godiya da mutanen da suka samu halarci duk da wahalar man da ake ciki
  • Gwamnatin jihar Legas ta bayyana bacin ranta kan wannan abu kuma ta gurfanar da ita a kotu

Legas - An gurfanar da Ms. Ogbulu Chindinma Pearl, a kotun laifuka na musamman dake unguwar Oshodi a jihar Legas kan laifin raba man fetur a taron biki.

Ogbulu Chindinma ta gurfana gaban Alkalin majistare, Kehinde Ogundare, ranar Litinin ne bisa zargin aikata laifuka hudu na jefa rayukan mutane cikin hadari ta hanyar raba jerkokin man fetur a taron bikin bata sarauta da akayi ranar 5 ga Maris, 2022.

Kara karanta wannan

Mu muka sace: An gurfanar da wasu mutane biyu da laifin satar taliya 'Spaghetti'

A cewar lauyoyin gwamnati, abinda tayi ya sabawa sashe na 251(1), 168 (1), 244 na dokokin jihar Legas, rahoton TheNation.

Biki a Legas
An gurfanar da matar da ta raba man fetur a wajen Biki a Legas Hoto: @thenation
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya kara da cewa an bada belinta kan Naira milyan biyu da kuma masu tsaya mata mutum biyu.

Alkalin kotun ya bada umurnin tabbatar da adireshin wadanda suka tsaya mata tare da tabbatar da cewa sun nuna takardun hujjar sun biya gwamnatin Legas haraji na tsawon shekaru uku da suka gabata.

An dage zaman zuwa ranar 24 ga Maris, 2022.

Wahalar Mai: Anyi rabon jarkokin man fetur a wani bikin jihar Legas

Kwanaki goma da suka gabata Yayinda yan Najeriya ke fama da matsanancin wahalar man fetur, mun kawo muku rahoton cewa an yi rabon jarkokin mai matsayin kyautar halartar biki a jihar Legas.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Gurfanar Da Tsohuwar Matar Fani-Kayode, Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama A Kotu

A hotunan da bidiyon da wani @ThisIsKennys ya saki a shafinsa na Tuwita, an kan yadda aka lika hotunan wanda ke bikin a jikin jarkuna da sunan "Erelu Okin Foundation Installation Party.”

Kalli bidiyon bikin:

Asali: Legit.ng

Online view pixel