Yadda Kwastoma Ta Yi Wa Mai PoS Wanka Da Miya Mai Zafi Saboda Data a Legas

Yadda Kwastoma Ta Yi Wa Mai PoS Wanka Da Miya Mai Zafi Saboda Data a Legas

  • ‘Yan sanda sun kama wata Blessing bisa watsa wa wata mai PoS, Bisola Kolawole miya mai zafi a shagon ta da ke wuraren Ikorodu cikin Jihar Legas
  • An samu bayanai akan yadda Blessing taje shagon Kolawole don siyan data ta N1,500 sai dai ta gaza amfani da datar a wayar ta wanda hakan ya hassala ta
  • Daga nan rikici ya barke har Blessing ta yaga mata kaya tare da balle mata sarkar zinaren ta wanda ta bi ta gida don ta bata sai ta watsa mata miya mai zafi

Legas - Wata Blessing tana hannun rundunar ‘yan sandan Jihar Legas bisa zargin ta da watsa wa wata mai Pos, Bisola Kolawole, miya mai zafi a unguwar Ikorodu da ke jihar.

Kara karanta wannan

Rabo a kan rabo: Baiwar Allah ta haifi yara biyu a lokaci daya, kuma ba tagawaye ba ne

The Punch ta tattaro bayanai akan yadda Blessing ta je shagon Kolawole da ke kan titin Igboolomu a Isawo-Agric don siyan data ta N1,500.

Yadda Kwastoma Ta Yi Wa Mai PoS Wanka Da Miya Mai Zafi Saboda Data a Legas
Kwastoma Ta Yi Wa Mai PoS Wanka Da Miya Mai Zafi Saboda Data a Legas. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Bayan ta biya kudin sai ta kasa amfani da datar a wayar ta. Lamarin ya kara tabarbarewa bayan Blessing ta yaga wa Kolawole kaya sannan ta balle mata sarkar zinaren ta.

Lokacin da Kolawole ta je amsar sarkarta a hannun Blessing ne ta watsa mata miya mai zafi

Yayin tattaunawa da wakilin The Punch a ranar Alhamis, ta ce ta je gidan kwastomar ta ta ne don ta amshi sarkar wacce ta yi layar zana inda Blessing ta watsa mata miya mai zafi.

Mazauna Jihar Ogun sun ce kirji da maman ta duk sun sulbe, wanda yasa aka zarce da ita babban asibitin Ikorodu don ta samu kular likitoci.

Kara karanta wannan

An Ba Wa Mele Kyari Wa’adin Kwana 7 Ya Kawo Ƙarshen Ƙarancin Man Fetur a Najeriya

Ta kara da cewa:

“Blessing ta aiki kanwar ta, Eniola don ta siyo mata data ta N1,500 daga wuri na a ranar Lahadi.
“Yayin da ta zo shagon sai ta samu mai tsaron shago na, Favour, wacce ta sanar da ni batun cinikin inda na yi gaggawar tura mata kuma kudi ya fita daga asusun banki na.
“Daga baya Blessing ta kira ni ta sanar da ni cewa data bata shigo mata ba. Na yi gaggawar kiran ma’aikatan banki inda suka ce matsala aka samu. Bayan Blessing ta kira ni na sanar da ita yadda muka yi da ma’aikatan bankin.”

Sai da Blessing taje har shagon ta inda ta kwashe mata kayan shago ciki har da na’urar PoS din ta

Ta ci gaba da labarta yadda tana kasuwa a ranar Litinin har Blessing ta tura mata sako ta wayar ta akan cewa har lokacin bata ga datar ba. Anan ta ci gaba da zagin ta.

Kara karanta wannan

Yadda Zainab Ta Gutsure Kunnen Masoyinta Saboda Ya Ba Ta N365 Matsayin Kuɗin Mota

Kolawole ta shawarci Favour ta sanya karafa don rufe shagon saboda gudun Blessing ta kai mata farmaki.

Washegari Blessing ta dawo ta dauki abubuwa a shagon ciki har da na’urar PoS din wanda yasa sai da mai shagon ta dakatar da ita.

A cewarta matar ta yaga mata kaya har ta yi mata tsirara tare da balle mata sarkar zinarenta wacce daga baya ta nema ta rasa.

Yayin da ta bi ta gida don yi mata korafi, ta shiga ciki, ta dauko miyar Egusi mai zafi ta watsa mata tare da amfani da almakashi wanda ta yankar mata hannu da shi.

Yayin da Kolawole ta yi yunkurin bin ta, sai ta yi gaggawar watsa mata sauran miyar a kirjin ta wanda ya ja aka yi saurin wucewa da ita asibiti.

Yanzu haka Blessing tana gidan gyaran hali

Bayan nan ne ‘yan sanda suka kama Blessing akan aika-aikar da ta yi.

Kara karanta wannan

Sai Miji Na Ya Lakaɗa Min Baƙin-Duka Sannan Yake Kwanciya Da Ni, Mata Ta Nemi Saki a Kotu

Mijin maman Blessing, Azeez Braimo, ya ce Kolawole ta nuna wa Blessing fin karfi ne shiyasa ita kuma ta watsa mata miyar don kare kan ta.

Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar, CSP Adekunle Ajisebutu ya ce an tura su kotu kuma Blessing zata ci gaba da zama a gidan gyaran hali.

Adamawa: Jarumin mai shago ya ragargaji ‘yan daba 2 da su ka yi kokarin fasa masa shago

A wani rahoton, kun ji wani mai shago, Mohammed Hamman Adama, ya nuna gwarzontakarsa bayan ya yi dambe da wasu yaran Shila yayin da su ka yi kokarin balle masa shagon sa da ke Sangere Bode a karamar hukumar Yola ta kudu a jihar Adamawa.

LIB ta ruwaito yadda aka tattaro bayanai akan wadanda ake zargin, Umar Sa’ad, mai shekaru 18 da Mohammed Idris, mai shekaru 20 suka lallaba shagon sa da misalin karfe 2:00 na daren 2 ga watan Satumban 2021 da addunan su, gudumomi, sanduna da sauran miyagun makamai.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

Bayan isar su shagon har sun fara balle kofar don su samu nasarar yasar shagon. Su na kici-kicin balle kofa mai shagon ya ji kara ya fita cikin sauri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel