Adamawa: Jarumin mai shago ya ragargaji ‘yan daba 2 da su ka yi kokarin fasa masa shago

Adamawa: Jarumin mai shago ya ragargaji ‘yan daba 2 da su ka yi kokarin fasa masa shago

  • Wani mai shago ya gwada jarumtar sa inda ya yi dambe da yaran Shila bayan sun yi kokarin fasa masa shagon sa a jihar Adamawa
  • Lamarin ya faru ne karfe 2:00 na dare a ranar 2 ga watan Satumban 2021 a karamar hukumar Yola ta kudu
  • Motsin su ya ji tun daga gida ya sharbo addar sa ya bi su, duk da dai sun datsa masa hannu, shima ya ji musu raunuka

Adamawa - Wani mai shago, Mohammed Hamman Adama, ya nuna gwarzontakarsa bayan ya yi dambe da wasu yaran Shila yayin da su ka yi kokarin balle masa shagon sa da ke Sangere Bode a karamar hukumar Yola ta kudu a jihar Adamawa.

LIB ta ruwaito yadda aka tattaro bayanai akan wadanda ake zargin, Umar Sa’ad, mai shekaru 18 da Mohammed Idris, mai shekaru 20 suka lallaba shagon sa da misalin karfe 2:00 na daren 2 ga watan Satumban 2021 da addunan su, gudumomi, sanduna da sauran miyagun makamai.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sanar min salon da suke bi wurin guje wa luguden sojin sama, Gumi

Adamawa: Jarumin mai shago ya ragargaji ‘yan daba 2 da su ka yi kokarin fasa masa shago
Hotunan 'yan daba da suka shiga shagon wani matashi a Adamawa. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Bayan isar su shagon har sun fara balle kofar don su samu nasarar yasar shagon.

Su na kici-kicin balle kofa mai shagon ya ji kara ya fita cikin sauri.

Kwatsam Mohammed ya ji karar shagon wanda dama kusa ne da gidan sa, ya lallabo da addarsa cikin sauri, kamar yadda LIB ta ruwaito.

Bayan hango shi da suka yi daya daga cikin su ya ranta a na kare yayin da dayan saboda tsabar karfin hali ya dauki adda ya nufo Mohammed.

Mai shagon ya samu nasarar sharba wa dan daban adda a hannun sa na hagu sannan dan daban ya datse sa da adda wanda hakan ya ja ya fita daga hayyacin sa jini ya hau kwarara.

Dan daban ya yi tunanin ya kashe mai shagon ne saboda jinin da ya yi ta kwarara

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Take anan dan daban ya tsere yana tunanin mai shagon ya mutu. Bayan jin hayaniyar ne ‘yan uwan mai shagon suka fito cikin sauri daga gida inda suka gan shi cikin jini sannan suka dauke shi aka garzaya dashi asibiti.

Washegari ‘yan sanda suka bi sawun jini har gidan wanda ake zargin a Sangare Bode aka kama shi tare da dan’uwan harkar sa.

Bayan gabatar dasu gaban kotun majistare ta daya dake Yola a ranar 10 ga watan Satumba saboda aiwatar da ta’addanci, balle wurin dake dauke da dukiya tare da cutar da wani bisa ganganci, wadanda ake zargin sun amsa laifukan su.

Bayan amsa laifukan su, Alkalin kotu , Aliyu Bawuro ya dage karar zuwa 23 ga watan Satumban 2021 don tabbatar da wasu shaidu sannan ya umarci a ajiye su a gidan gyaran hali.

Wani mutum ya gamu da ajalinsa yayin da ya shiga maƙabartar musulmi cikin dare don haƙo gawa

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Afghanistan ya nemi afuwar mutanen ƙasar kan tserewar da ya yi Dubai ya bar su hannun Taliban

A wani labarin daban, wani mutum da ba a gano ko wanene ba ya mutu yayin da ya ke yunkurin hako gawa a makabarta da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, Premium Times ta ruwaito.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a makabartar musulmi da ke Iberekodo, karamar hukumar Abeokuta ta Arewa na jihar Ogun.

Abimbola Oyeyemi, mai magana da yawun yan sandan jihar Ogun, ya tabbatarwa Premium Times afkuwar lamarin a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel