Sarkin da ya fi kowa kudi a Najeriya (Kuma ba Sarkin Kano Sanusi II bane)
– Mujallar Forbes ta bayyana arzikin Sarakunan Najeriya
– An dai sha gaban Sarkin Musulmi da Sarkin Kano
– Sarkin da ya fi kowa dukiya shine Sarkin Kasar Ugbo
Za ka yi mamaki ka ji cewa ba Sarkin Kano bane ya fi kowa arziki a Najeriya
Duk da Sarkin yayi Gwamnan babban bankin kasar akwai wadanda su ka kera shi
Sarki Fredrick Obateru ne ya fi kowa dukiya cikin Sarakuna
Sarkin Kasar Ugbo da ke Kudancin Najeriya mai martaba Fredrick Obateru Akinruntan ne ya fi kaf Sarakunan Najeriya dukiya kamar yadda Jaridar Forbes ta bayyana. Mai martaban ya mallaki sama da Dala Miliyan 300.
KU KARANTA: Dangote ya fara ciyar da Jama'an Maiduguri
Wanda ya zo na biyu kuma dai shi ne Ooni watau Sarkin Kasar Ife Oba Sijuade wanda shi ma ya ba sama da Dala Miliyan 75 baya. Sarkin kasar Ife dai yana da kamfanin gine-gine inda kuma mai martaba Obateru Akinruntan ya maida hankali wajen harkar mai.
Mujallar Forbes ta fitar da wadanda su ka fi kowa albashi cikin ‘Yan wasa inda ku ka ji cewa Dan wasa Cristiano Ronaldo dai ya kerewa kowa a maganar kudi.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Akwai yiwuwar a raba kasar Najeriya
Asali: Legit.ng