Yakin Rasha da Ukraine: Kamfanin Google ya sanya wa Rasha takunkumi mai tsanani

Yakin Rasha da Ukraine: Kamfanin Google ya sanya wa Rasha takunkumi mai tsanani

  • Kamfanin Google ya shiga cikin jerin kamfanonin da ke daukar tsauraran matakai kan Rasha da shugaba Vladimir Putin saboda mamayar soja a kasar Ukraine
  • Kamfanin fasahar na kasa-da-kasa ya dakatar da duk wani nau'in tallace-tallace a Rasha bayan da kasar ta ke ci gaba da rikici da Ukraine
  • Tun da farko Google ya dakatar da RT, Sputnik da sauran kafofin watsa labarai da gwamnatin Rasha ke daukar nauyinsu a YouTube a Turai yayin yakin da ke kara ta'azzara

Kamfanin fasaha na Google a Amurka kuma katafaren dandalin bincike na yanar gizo, ya dakatar da duk wani nau'in talle da 'yan Rasha ke yi, a daidai lokacin da Shugaba Vladimir Putin ya fara yakar kasar Ukraine.

Jaridar New York Times ta ruwaito cewa Google ya sanar da dakatarwar ne a daren jiya Alhamis 3 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Rukunin farko na yan Najeriya mazauna Ukraine sun iso Abuja

Kamfanin Google ya sanyawa Rasha takunkumi
Da dumi-dumi: Kamfanin Google ya cire tsarin tallace-tallacensa a kasar Rasha | Hoto: aljazeera.com
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa kamfanin ya dauki wannan mataki ne bayan da hukumar kula da harkokin intanet ta kasar Rasha ta umarce shi da ya daina nuna tallace-tallacen da suke nuna bayanan karya game da mamayar kasar Ukraine.

Google ya ce ya dakatar da kasuwancinsa na talla a Rasha, ciki har da binciken yanar gizo, YouTube da harkokin tallace-tallacen yanar gizo, kamar yadda Reuters ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A baya dai kamfanin ya dakatar da dukkan tallan abubuwan da kafafen yada labaran kasar Rasha suka samar.

Ya bayyana cewa tuni ya toshe tallace-tallacen da ke da alaka da rikicin saboda ba sa son mutane su yi amfani da rikicin don samun kudi.

Kamfanin ya fitar da sanarwa, inda yace:

"Bisa la'akari da yanayi na musamman, mun dakatar da tallace-tallacen Google a Rasha. Yanayin yana ta'azzara cikin sauri, kuma za mu ci gaba da ba da sabbin bayanai a lokacin da ya dace."

Kara karanta wannan

Yana Da Katafaren Fada A Cikin Daji: Abubuwa 4 Masu Mamaki Game Da Shugaban Rasha Vladimir Putin

An haramtawa Magen Rasha shiga gasar wasanni bisa mamayar Ukraine

A wani labarin, kungiyar Mage ta Duniya ta ce ta haramtawa Magunan Rasha shiga gasarta a matsayin ladabtar da Shugaba Vladimir Putin bisa farmakar Ukraine, The Cable ta ruwaito.

A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, kungiyar - wacce ke alfahari da kanta a matsayin "Kungiyar Majalisar Dinkin Duniya ta Maguna" - ta ce "ta firgita kuma ta jijjiga" da ta ji cewa sojojin Rasha za su mamaye Ukraine tare da "fara yaki."

Kungiyar da ke Faransa - wacce kuma aka sani da Fédération Internationale Féline (FIFe) - ta ce ta yanke shawarar ne a ranar Talata, saboda ba za ta iya ganin wannan ta'asa ba kuma ba ta yi komai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel