Cikakken bayani: Batiri ya jawo gini a ma'aikatar kudin Najeriya ya kama da wuta

Cikakken bayani: Batiri ya jawo gini a ma'aikatar kudin Najeriya ya kama da wuta

  • Da sanyin safiyar yau Laraba ne aka samu labarin tashin gobara a ma'aikatar kudi ta tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja
  • Rahotanni sun ce, an ga alamun hayaki daga ginin ma'aikatar, kana jami'an hukumar kashe gobara sun hallara
  • Kakakin rundunar kashe gobara ta tarayya ya tabbatar da faruwar lamarin, hakazalika ma'aikatar ilimi ta yi bayanin abin da ya faru

FCT, Abuja - Wani ginin Ma’aikatar Kudi ta Tarayya da ke tsakiyar babban birnin tarayya Abuja na ci da wuta a halin yanzu, inji rahoton Leadership.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, an ga jami’an kashe gobara sun iso wurin domin kashe gobarar.

Gobara ta kama a ma'aikatar kudi
Yanzu-Yanzu: Gini a ma'aikatar kudin Najeriya da ke Abuja ya kama da wuta
Asali: Original

Jaridar Punch ta ce, kakakin hukumar kashe gobara ta tarayya, Abraham Paul, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce a halin yanzu jami’an hukumar na ci gaba kokari kashe gobarar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin tarayya ta sa labule da kungiyar ASUU a Abuja

Ma'aikatar kudi ta magantu

Sai dai, da ma'aikatar kudi ta tarayya ke martani game faruwar gobarar, ta bayyana cewa, ba dukkan ma'aikatar bane ta kama da wuta, face dai wani bangare na ginin kasa a ma'aikatar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, sanarwar ta bayyana musabbabin tashin gobarar, inda aka ce batiri ne ya jawo tashin wuta.

A wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar dauke da sa hannun mashawarci na musamman ga ministar kudi kan harkokin yada labarai, ce:

“Hedkwatar ma’aikatar kudi ta tarayya ba ta kama da wuta ba kamar yadda aka yayata a shafukan sada zumunta."

Mashawarcin, Yunusa Tanko Abdullahi ya yi bayanin cewa, wani yanki ne na ma'aikatar da ke dauke da wani nau'in batiri ya kama da wuta, kuma an samu nasarar kashe wutar cikin gaggawa.

Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani gida, uwa da jaririnta sun kone a Kano

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu ta amince da bukatar NDLEA kan Abba Kyari da sauran mutum 6

A wani labarin, hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wani yaro mai suna Sulaiman Usaini dan shekara daya da mahaifiyarsa mai suna Zainab Yusha’u mai shekaru 25 a hanyar Gwarzo da ke Gidan Kaji a jihar Kano.

Alhaji Saminu Abdullahi, jami’in hulda da jama’a na hukumar ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Kano, Daily Trust ta ruwaito.

Abdullahi ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar Asabar 8 ga watan Janairun 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel