Da Dumi-Dumi: Kotu ta amince da bukatar NDLEA kan Abba Kyari da sauran mutum 6

Da Dumi-Dumi: Kotu ta amince da bukatar NDLEA kan Abba Kyari da sauran mutum 6

Abuja - Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abuja, ranar Talata, ta amince da bukatar da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta shigar kan Abba Kyari da abokan harkallarsa 6.

Vangurad ta tattaro cewa hukumar NDLEA ta shigar da bukatar neman izinin Kotu na cigaba da tsare Kyari da sauran mutum shida na tsawon mako biyu.

Hukumar ta shaida wa kotun cewa, mutane da take neman izinin cigaba da tsare su, na fuskantar bincike kan zargin hannu a fataucin miyagun kwayoyi zuwa Najeriya.

Shugaban lauyoyin NDLEA, wanda ya shigar da bukatar gaban Kotu. ya ce hukumar na bukatar karin lokaci domin gudanar da bincike a tsanake kan duk masu hannu a lamarin.

Daga cikin waɗan NDLEA ta bukaci tsare wa, har da mutum biyu da ke aiki tare da Abba Kyari, Chibunna Patrick Umeibe da kuma Emeka Alphonsus.

Kara karanta wannan

An gurfanar da mata 3 kan laifin jika AlKur'ani da jinin biki da jefawa cikin masai a Zamfara

Matakin da Kotu ta ɗauka

Bayan sauraron koken lauyan NDLEA da bukatar da lauyan ya shigar, Alkalin Kotun, Mai Shari'a Zainab Abubakar, ta amince da bukatar na take.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel