Gwamnatin tarayya zata gana da manyan Malaman addini kan yajin aikin ASUU, Ngige

Gwamnatin tarayya zata gana da manyan Malaman addini kan yajin aikin ASUU, Ngige

  • Gwamnatin tarayya zata shirya zama da Sarkin Musulmai da Shugaban CAN don shawo kan ASUU
  • Majalisar shugabannin addinai a Najeriya NIREC ta baya ta zauna da ASUU don kwantar da kuran yajin aiki
  • ASUU ta bayyana cewa ta fahimci yaudara ce ta gwamnatin tarayya, bata shirya biyan bukatunta ba

Ministan Kwadago, Dr Chris Ngige, ya bayyana cewa zai shirya zama tsakanin manyan masu ruwa da tsaki kan ganin yadda za'a kawo karshen yajin aikin Malaman jami'o'in Najeriya ASUU.

Punch ta ruwaito cewa Ngige, wanda yayi tafiya kasar waje yace yana dawowa Najeriya makon gobe zai shirya zaman sannan su tuntubi shugabannin ASUU.

Chris Ngige
Gwamnatin tarayya zata gana da manyan Malaman addini kan yajin aikin ASUU, Ngige Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Hotunan manyan yan Kannywood yayin da suka gana da mataimakin shugaban kasa a Villa

Wadanda Ngige yace zasu halarci taron sune shugabannin majalisar shugabannin addinai NIREC wanda ya hada da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar; da Shugaban kungiyar CAN, Rabaran Samson Ayokunle.

Hakazalika akwai Ministan Ilmi, Adamu Adamu; Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, da sauran su.

Ngige yace:

"Kamar yadda na fadi a baya, mun yi mamakin shiga yajin ASUU duk da cewa sun fadawa NIREC zasu je su tattauna da shugabanninsu. Yaynda suke sauraron yadda sukayi muka samu labarin sun shiga yajin aiki."
"Amma idan na dawo kasar ranar Lahadi. Zan shirya taro da NIREC, Ministan Ilmi, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, sannan mu tuntubesu (ASUU)."

Kafin magana ta yi nisa, Ministan ilimi na neman biyan bukatar kungiyar ASUU

A wani labarin, ma’aikatar ilmi ta tarayya ta fara kokari na ganin ta biya wani daga cikin bukatun da kungiyar malaman jami’a watau ASUU suka zo da shi.

Jaridar Punch ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta na shirin aiki da rahoton kwamitocin da shugaban kasa ya nada domin su yi bincike a jami’o’in.

Kara karanta wannan

Mu ma nan ba da dadewa ba da yiwuwan mu shiga yajin aiki, Kungiyar Malaman Poly ASUP

Darektan yada labarai na ma’aikatar ilmi, Ben Goong ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

ASUU ta dauki sama da shekara daya tana sauraron gwamnatin Muhammadu Buhari ta cika wannan alkawari da aka yi mata kafin ta dawo aiki a 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel