'Karin bayani: Yan ta'adda a Kaduna sun datse wa mutane 2 gaɓoɓi, sun sace 22 sun kuma raunata 4

'Karin bayani: Yan ta'adda a Kaduna sun datse wa mutane 2 gaɓoɓi, sun sace 22 sun kuma raunata 4

  • Wasu miyagun yan ta'adda sun kai hari a Idon a karamar hukumar Kajuru a Kaduna inda suka yi garkuwa da mutane 22
  • Sun kuma raunta wasu mutanen garin biyu a harin da suka kai cikin dare inda suka rika harbe-harbe da bindiga
  • Bala Jonathan, Kansila a karamar hukumar Kajuru ya lissafa sunayen wadanda aka sace, ya bada sunan wadanda suka jikkata

Kaduna - Yan ta'adda a Jihar Kaduna sun yi garkuwa da mutane 22 sun kuma raunata wasu a ranar Laraba a garin Idon da ke karamar hukumar Kajuru a jihar, Vanguard ta ruwaito.

Hakazalika, Yan sanda a Jihar Kaduna sun ce jami'ansu sun kama hatsabiban yan bindiga 2 da suka datse wa wadanda suka sace sassan jiki, kusa da kauyen Sabon-Gaya a karamar hukumar Chikun a babban hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Kisan Hausawa dillalan shanu a Kudu: Kungiyoyin Arewa sun fusata, sun tura gargadi ga gwamnatin Abia

Da Duminsa: Yan ta'adda sun datse wa mutane 2 gabobi, sun sace 22 sun kuma raunata 4 a Kaduna
Yan ta'adda sun datse wa mutane 2 gabobi, sun sace 22 sun kuma raunata 4 a Kaduna. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Amma, yan sandan ba su yi magana ba game da mutanen 22 da aka sace a Kajuru.

A cewar mutanen yankin da abin ya faru, "batagarin sun zo ne misalin karfe 12.30 na daren Laraba a lokacin da mutanen garin ke barci."
"Sun fara harbe-harbe da bindiga, suka balle kofofi da tagogi suka kwashi mutane zuwa daji."
"Ba mu san ta yadda suka zo ba kawai mun ji harbi ne suna fasa taga da kofofi. Sun zo misalin karfe 12.30 na dare."

Sunayen wadanda aka sace da wadanda aka yi wa rauni

Kansila a karamar hukumar Kajuru ya lissafa sunayen wadanda aka sace, Bala Jonathan ya bada sunan wadanda aka sace da wadanda aka yi wa rauni.

A cewarsa bayan harin, wanda aka sace sune:

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An sake yi wa matafiya 'yan Kano da Nassarawa kisar gilla a hanyar Jos

"Justina Joseph, Mary Joseph, Rejoice Joseph, Stephen Joseph Samson Ladan, Christiana David, Boniface David, Helen Aminu, Mirabel Aminu, Precious Philemon, Nelson Philemon, Christian Philemon.”
"Saura sun hada da Yosi Gabriel, Stephen Clement, Jinkai Musa, Derrick Obadiah, Daniel David, Paul David, Istifanus Peter, Miracle Matthew, Jesse Charles da Favour Daniel .”
Wadanda aka yi wa raunin sune David Maigaya, Micah Musa, Josephine Matthew da Marshall Musa.”

'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel