Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Ɗaurin Watanni 18 a Ranar Valentine Kan Yaudara Da Sunan Soyayya

Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Ɗaurin Watanni 18 a Ranar Valentine Kan Yaudara Da Sunan Soyayya

  • Kotu ta yanke wa wani mutum dan shekaru 25 daurin watanni 18 a gidan gyaran hali kan yaudarar soyayya
  • An yanke wa matashin hukuncin ne a wata babban kotun Jihar Osun a ranar 14 ga watan Fabrairu wato ranar masoya 'Valentine'
  • Wanda ake zargin ya amsa laifinsa an kuma kwato wayarsa ta salula na Iphone 6 an ajiye a baitul malin gwamnatin tarayya

Ilorin - Mai Shari'a Mohammed Sani na babban kotun tarayya a Ilorin, a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairun 2022, ya samu wani matashi mai shekaru 25, Olaleye Paul daga karamar hukumar Odo-Otin a Jihar Osun ta laifi ya yanke masa daurin wata 18 kan laifuka masu alaka da damfara ta intanet.

Olaleye na daga cikin wadanda ake zargi da aka kama a Ogbomosho, Jihar Oyo, a ranar 26 ga watan Oktoban 2021, bayan samun bayanan sirri kan wasu da ake zargin yan damfara ne da EFCC ta kama a Ilorin, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Naɗa Mohammed Bello Koko a Matsayin Shugaban NPA Mai Cikakken Iko

Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Ɗaurin Watanni 18 a Ranar Valentine Kan Yaudara Da Sunan Soyayya
An yanke wa wani daurin watanni 18 a gidan gyaran hali saboda yaudara da sunan soyayya. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tuhumar da aka karanto masa:

"Kai, Olaleye Olumide Paul, a watan Maris din 2019 a Ogbomosho ka yo sojan gona a matsayin wani Roven Riley ta hanyar amfani da beautifullina@gmail.com da nufin samun $154.82 (Dallar Amurka Dari da Hamsin da Hudu) hakan laifi ne da ya ci karo da sashi na 22(3) na dokar hana damfarar intanet ta 2015 da hukuncinta ke sashi na 22(3)."

Wanda ake zargin ya amsa laifinsa

Bayan karanto tuhumar da aka masa, lauyan EFCC, Sesan Ola ya yi jawabi kan shari'ar ya kuma gabatar da kalaman da wanda ake karar ya yi a rubuce da wayarsa ta Iphone 6 da aka kwato yayin kama shi.

Ola ya bukaci kotun ta yanke hukunci ko da wanda ake karar bai bayyana a kotu ba.

Kara karanta wannan

Tsohon kwamishinan Zamfara Danmaliki ya koka, ya ce ana barazana ga rayuwarsa

Hukuncin da alkali ya yanke

Bayan sauraron karar, Mai Shari'a Sani ya samu wanda ake karar da laifi bisa tuhumar uku da ake masa.

Ya yanke masa hukuncin daurin wata shida kan kowanne laifin daya, za a kidaya su tare sannan ya bada zabin biyan tarar N100,000 a kan kowanne tuhuma.

Kotun ta kuma bada umurnin a karbi wayan Iphone 6 din a saka baitul malin gwamnatin tarayya, sannan wanda ake zargin zai biya $504 ga wadanda aka yaudara.

Hotunan mutumin da aka kama ya damfari mutane 64 miliyoyin naira a Kano

A wani rahoton daban, Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani hatsabibin dan damfara bisa zargin sa da amfani da sunan babban bankin Najeriya wurin yasar dukiyar mutane 64 ta hanyar amfani da takardun bogi, LIB ta ruwaito.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Laraba, 8 ga watan Satumba inda yace an kama wanda ake zargin, Buhari Hassan a Yankaba Quarters ne da ke jihar.

Kara karanta wannan

Karfin hali: EFCC ta kwamushe wani mutum da ke ikirarin shi PA ne na gwamnan jiha

Asali: Legit.ng

Online view pixel