Hotunan mutumin da aka kama ya damfari mutane 64 miliyoyin naira a Kano

Hotunan mutumin da aka kama ya damfari mutane 64 miliyoyin naira a Kano

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta damki wani mashahurin dan damafara mai amfani da sunan babban bankin Najeriya (CBN) wurin warwarar kudin jama’a
  • Rundunar ta kama Buhari Hassan a Yankaba Quarters a ranar Laraba, 31 ga watan Augustan 2021 bayan ya damfari mutane 64 miliyan 6 da doriya
  • Bayan ya ji lugude ya bayyana cewa kawai salo ne da ‘yan damfara da son tatsar dukiya a hannun jama’a don har takardun bogi yake hada wa da kanshi

Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani hatsabibin dan damfara bisa zargin sa da amfani da sunan babban bankin Najeriya wurin yasar dukiyar mutane 64 ta hanyar amfani da takardun bogi, LIB ta ruwaito.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Laraba, 8 ga watan Satumba inda yace an kama wanda ake zargin, Buhari Hassan a Yankaba Quarters ne da ke jihar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun far ma matafiya, sun yi garkuwa da mutum 5 a Ondo

Hotunan mutumin da aka kama ya damfari mutane 64 miliyoyin naira a Kano
Mutumin da aka kama ya damfari mutane 64 a Kano. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hotunan mutumin da aka kama ya damfari mutane 64 miliyoyin naira a Kano
Mutumin da yan sanda suka kama bisa damfara a Kano. Hoto: LIB
Asali: Facebook

A cewarsa:

“A ranar 31 ga watan Augustan 2021, da misalin karfe 3pm muka samu rahoto akan wani Buhari Hassan mai shekaru 37 mazaunin Kawaji Quarters da ke karkashin karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano wanda yake ikirarin shi jami’i ne na kungiyar audugar Najeriya da ke karkashin babban bankin Najeriya (CBN) kuma yana bayar da rancen kudade ne. Da hakan ya damfari mutane da dama ta hanyar nuna musu takardun bogi.”

A cewar rahoton na LIB, Bayan samun rahoton ne kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya umarci jami’an sa wanda ya sa SP Shehu ya jagorance su kamo wanda ake zargin.

Kakakin hukumar ya ce basu yi kasa a gwiwa ba suka nufi har Yankaba Quarters da ke Kano bayan ya amshi N700,000 a hannun wasu Muttaka Muhammad da Habibu Muhammad duk ‘yan karamar hukumar Nasarawa.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun halaka mutum daya tare da jikkata wani a jihar Bauchi

An samu katika a hannun sa masu sunaye daban-daban da hotuna a jikin su na mutane 47 da sauran takardun bogi na kungiyar audugar Najeriya bangaren Kano. Bayan ci gaba da bincike ne aka gano cewa shi da kan shi yake hada takardun na bogi.

Mutumin ya ce ta bada aiki da Kungiyar Auduga ta Nigeria

Hotunan mutumin da aka kama ya damfari mutane 64 miliyoyin naira a Kano
Shaidar aiki da kungiyar auduga da aka samu hannun dan damfara a Kano. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Lokacin da ya ji lugude ya bayyana cewa ya taba aiki da kungiyar Audugar Najeriya amma an fatattake shi bayan an kama shi ya kirkiro wasu takardu na bogi. Ya kuma bayyana cewa damfara ce kawai yake yi wa jama’a.

“A kalla mutane 64 ne suka kawo korafi akan yasar kudaden su da ya yi, N6,294,200 da ya yi.
"Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko (Nagari-Nakowa) ya bayar umarnin ci gaba da binciken wanda ake zargin. Kuma ana kammalawa za a tura shi kotu don a yanke masa hukunci,” kamar yadda takardar ta zo.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta kori Gwamna Buni a matsayin shugaban riko na APC, ta dakatar da taron karamar hukuma

Jigawa: Hotunan Auren Yaya Da Ƙanwa da Kotun Shari’ar Musulunci Ta Aurar da Su Duk da Ƙin Amincewar Mahaifinsu

A wani labarin daban, wata babban kotun Shari'a a ƙaramar hukumar Hadejia na Jihar Jigawa, a ranar Alhamis, ta aurar da wasu mata biyu ƴaƴa da ƙanwa, Premium Times ta ruwaito.

An aurar da matar biyu ne bayan mahaifinsu, Abdullahi Malammmadori, ya ƙi aurar da su duk da wa'adin kwanaki 30 da kotun ta bashi amma bai aurar da su ba.

Shugaban wata gidauniya na taimakon mata, marayu da marasa galihu, Fatima Kailanini, ta yi ƙarar Mr Malammadori kan ƙin aurar da Khadijat da Hafsat Abdullahi duk da sun fito da waɗanda suke so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel