Wata sabuwa: Ana barazanar daina Facebook da Instagram a Turai saboda dalilai

Wata sabuwa: Ana barazanar daina Facebook da Instagram a Turai saboda dalilai

  • Akwai yiwuwar dakatar da ayyukan Facebook da Instagram a duk fadin Turai idan barazanar da Meta ta yi ya tabbata
  • Kamfanin ya ce idan ba a ba shi tabbacin ikon ci gaba da mika bayanai ga gwamnatin Amurka ba ba shi da wani zabi illa rufe ayyukansa
  • EU tana tsara sabuwar doka game da mika bayanai wanda ya sabawa babban kamfanin fasahar tare da 'yan majalisa da ke cewa Meta yana son murkushe su

Bayan buga wani mummunan aiki na kudi a makon da ya gabata, Meta, uwa ga manhajojin Facebook da Instagram, ya ce yana iya rufe manhajojin a Turai saboda rashin jituwar mika bayanai.

Ta ce tana iya rufe shafukan idan ba za a ba ta damar ci gaba da mika bayanan 'yan yankin Turai ga gwamnatin Amurka ba.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnatin Niger ta saka dokar hana fita a kananan hukumomi 2

Kamfanin fasahar zamani na Meta zai janye daga Turai
Wata sabuwa: Ana barazanar daina Facebook da Instagram a Turai saboda dalilai | Hoto: businessday.ng
Asali: Getty Images

Kamfanin manhajojin sada zumunta ya bayar da wannan gargadi na rufe wa ne a ranar Alhamis, 3 ga Fabrairu, 2022, a cikin rahotonsa na shekara, kamar yadda EuroNews ta ruwaito.

Hukumomin Turai suna tsara wata doka da za ta nemi a nuna yadda ake mika bayanan mazauna nahiyar Turai zuwa kasar Amurka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Me Facebook ke cewa

Facebook ya ce idan ba a amince masa kan sabon tsarin raba bayanai ba to ba zai iya ci gaba da dogaro da tsarin Standard Contractual Clauses (SCCs) ba ko kuma dogaro da wasu ka'idojin musayar bayanai daga kasashen EU zuwa Amurka ba.

Wannan ke nuni da cewa, idan batutuwan basu daidaita ba tsakanin dokar Amurka da ta EU, to dole Facebook da Instagram su daina aiki a Turai.

Katafaren kamfanin na fasaha ya ce hakan zai yi tasiri a zahiri da kuma zai iya zama illa ga kasuwancinsa, yanayin shigar kudi da sakamakon ayyukansa.

Kara karanta wannan

Duk a cikin so ne: Saurayi ya kaftawa budurwarsa mari sannan ya roki ta aureshi

Dan majalisar EU ya yi martani game da maganar

Wani dan majalisar dokokin Turai, Axel Voss ya fada a shafinsa na Twitter cewa ba zai yiwu Meta ta bata EU ba wajen cika ka'idojin kare bayananta. Voss ya kara da cewa idan Meta ya fice daga EU, to zai zama hasarar kamfanin na Meta.

A cewar mai magana da yawun Meta, kamfanin ba shi da sha'awar rufewa da janjewa daga nahiyar Turai amma ya bayyana wasu damuwowi a cikin abubuwan da suka gabata, in ji rahoton CNBC.

Facebook, WhatsApp da Instagram sun daina aiki

A watannin baya, manhajojin Facebook, WhatsApp da Instagram sun daina aiki a fadin duniya da yammacin yau Litnin, 4 ga Satumba, 2021.

Manhajojin uku - Mallamin kamfanin Facebook suna amfani da kayan aiki daya ne kuma suka daina aiki gab da karfe 5 na yamma.

Masu ziyartar Shafin sun bayyana cewa kawai shafukan sun daina aiki ne.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Dan KASTLEA ya kashe direban mota da duka a Kaduna

Asali: Legit.ng

Online view pixel