Da dumi-dumi: Facebook, WhatsApp da Instagram sun daina aiki
- A wani abun da ba'ayi zato ba, manyan manhajojin ra'ayi da sada zumunta sun daina aiki
- Wannan ba shi ne karo na farko da wannan abu zai faru ba
- Kamfanin Facebook ta bada hakuri ga al'ummar duniya kan wannan abu
Manhajojin Facebook, WhatsApp da Instagram sun daina aiki a fadin duniya da yammacin yau Litnin, 4 ga Satumba, 2021.
Manhajojin uku - Mallamin kamfanin Facebook suna amfani da kayan aiki daya ne kuma suka daina aiki gab da karfe 5 na yamma.
Masu ziyartar Shafin sun bayyana cewa kawai shafukan sun daina aiki ne.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Me ya faru?
Wani mai magana da yawun kamfanin, Andy Stone, ya bada hakuri ga daukacin mabiyansu amma bai bayyana ainihin abinda ya faru ba, cewar jaridar Independent.
Yace:
"Muna sane da cewa mutane na fuskantar matsala wajen amfani da manhajojinmu. Muna kokarin gyara kuma muna bada hakuri."
Hakazalika an daura irin wannan jawabi a shafin Facebook na manhajar Tuwita.
Manhajar Instagram ma ta bada nata hakurin inda tace:
"Instagram da jama'arta na fuskantar matsala yanzu. Kuyi hakuri da mu, muna aiki kai."
Ita ma manhajar Whataspp a shafinta na Tuwita ta bada irin wannan hakuri.
Asali: Legit.ng