Kotu ta saki wani tela bayan ya yi shekaru 3 a gidan gyaran hali yana jiran shari'a

Kotu ta saki wani tela bayan ya yi shekaru 3 a gidan gyaran hali yana jiran shari'a

  • A ranar Juma’a Justice Oluwatoyin Taiwo ta kotun laifuka na musamman da ke Ikeja ta saki Femi Kazeem, tela mai shekaru 32 wanda aka daure a gidan gyaran halin Kirikiri bisa zargin sa da fashi da makami
  • An zargi Kazeem da fashin wayar wani mutum ne yayin da ya yi amfani da wani karfe sai kuma aka zarge shi da yi wa wata mata fashin jaka daga hannun ta a ranar 28 ga watan Augustan 2018
  • Alkalin ta saki Kazeem ne saboda masu karar sun kasa gabatar da shaidoji bayan lauyan mai kara, O. A. Bajulaiye-Bishi ya ce ba a ga daya daga cikin shaidun ba dayan kuma ba ya da ra’ayin bayar da shaidar

Legas - Mai Shari'a Oluwatoyin Taiwo ta kotun laifuka na musamman ta saki wani tela, Femi Kazeem, mai shekaru 33 a ranar Juma’a bayan ya kwashe shekaru 3 a gidan gyaran halin Kirikiri bisa zarginsa da fashi da makami.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano

An zargi Kazeem da kwatar wayar wani mutum yayin da ya yi amfani da karfe. Sannan an kara zargin sa da kwatar jakar wata mata, Premium Times ta ruwaito.

Kotu ta saki wani tela bayan ya yi shekaru 3 a gidan gyaran hali yana jiran shari'a
Alkali ta saki wani tela bayan ya kwashe shekaru 3 a gidan gyaran hali yana jiran shari'a. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

NAN ra ruwaito yadda alkalin ta saki Kazeem saboda masu kara sun kasa gabatar da shaidu akan sa.

Daya daga cikin shaidun ba ya da ra’ayin ci gaba da bayar da shaida

Lauyan mai kara, O. A. Bajulaiye-Bishi ta sanar da alkalin cewa daya daga cikin shaidun ba ya da ra’ayin ci gaba da bibiyar karar yayin da aka kasa sanin inda dayan yake.

Kamar yadda ta shaida wa kotu:

“Shaidan da aka sace wa wayar ya ce wayar hannu ce kacal kuma yanzu haka ya mallaki wata.”

Ganin haka lauyan wanda ake kara, A. K. Chalokwu ya bukaci kotun ta yi watsi da karar kuma ta sallami wanda ake zargin.

Kara karanta wannan

Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105

Alkalin ta saki Kazeem kasancewar babu kwararan shaidu

Yayin sakin Kazeem, Mrs Taiwo ta ce:

“Duk da dai ana zargin sa da fashi da makami, amma na karkata akan bukatar lauyan wanda ake kara.
“Hakan ya sa na saki wanda ake kara kamar yadda sashi na 232(3) na dokar Criminal Justice ta 2021 wacce aka gyara ta tanadar.”

Bayan jin hakan ne Kazeem ya daga hannu yana murna tare da durkusa wa alkalin. Lauyan sa ya nuna godiyar ga kotun da kuma farin cikin sa mara misaltuwa, rahoton Premium Times.

A cewar lauyan mai kara, Kazeem ya yi laifin ne a ranar 28 ga watan Augustan 2018 a tashar motar Ejigbo da ke Isolo a Jihar Legas.

Ta kara da cewa:

“Wanda ake kara ya kwace wayar wani Prince Jombo ne, kirar Infinix Hot 5 wacce tsadar ta ta kai N39,500. Sannan ya kwace jakar wata mata wacce akwai N40,000 a cikin ta.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan awaren IPOB suka halaka makiyayi, suka bindige shanu 30

“Laifin ya ci karo da sashi na 297(2)(a) na Criminal Law ta Jihar Legas ta shekarar 2015.”

Ba zan iya ba: Jarabar mijina ta yi yawa, yana so ya kashe ni da saduwa, Matar aure ga kotu

A wani labarin, wata matar aure mai 'ya'ya uku, Olamide Lawal, a ranar Juma'a ta roki kotun Kwastamare da ke zamansa a Mapo, Ibadan, ya raba aure tsakaninta da mijinta, Saheed Lawal, saboda yana jarabar ta da yawan saduwa, rahoton Premium Times.

A karar da ta shigar, Olamide wacce ke zaune a Ibadan ta kuma yi ikirarin cewa mijinta ya saba shan giya ya yi tatil yana maye, The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel