Ba zan iya ba: Jarabar mijina ta yi yawa, yana so ya kashe ni da saduwa, Matar aure ga kotu

Ba zan iya ba: Jarabar mijina ta yi yawa, yana so ya kashe ni da saduwa, Matar aure ga kotu

  • Olamide Lawal, wata matar aure mai yara uku, ta garzaya kotu tana neman a datse igiyan aurenta da mijinta, Saheed Lawal
  • Olamide ta koka da cewa mijinta ba shi da aikin yi sai shan giya ya yi tatul, tare da dukanta da tilasta mata kwanciya da shi ba kakautawa
  • A bangarensa, mijin matar, Saheed Lawal ya roki kotun ta taya shi tattausa zuciyar matarsa yana mai cewa ya tuba kuma zai sauya halayensa

Ibadan - Wata matar aure mai 'ya'ya uku, Olamide Lawal, a ranar Juma'a ta roki kotun Kwastamare da ke zamansa a Mapo, Ibadan, ya raba aure tsakaninta da mijinta, Saheed Lawal, saboda yana jarabar ta da yawan saduwa, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Buhari: PDP za ta kwace mulki daga hannun APC idan har bata magance rikice-rikicenta ba

A karar da ta shigar, Olamide wacce ke zaune a Ibadan ta kuma yi ikirarin cewa mijinta ya saba shan giya ya yi tatil yana maye, The Nation ta ruwaito.

Ba zan iya ba: Jarabar mijina ta yi yawa, yana so ya kashe ni da saduwa, Matar aure ga kotu
Jarabarsa ta yi yawa, a raba mu kafin ya kashe ni, Matar aure ta fada wa kotu. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce:

"Mun shafe shekaru 14 muna zaman aure da Lawal. Tantirin mashayin giya ne kuma ba shi da tausayi ko kadan a zuciyarsa.
"Abin da ya mayar da hankali a kai shine shan giya, duka na da kuma tilasta min kwanciyar aure da shi. Baya kulawa da yaran mu.
"Ba zan iya cigaba da zama tare da shi ba."

Lawal ya roki kotu ta bashi dama ya yi sulhu da matarsa

A bangarensa, Lawal ya roki kotun ta taimaka ta bawa matarsa hakuri domin ta cigaba da zama da shi.

Lawal, wanda sana'ar dinki ya ke yi ya ce:

Kara karanta wannan

Buhari: Tsufa ya fara nuna wa a jiki na amma dai nagode wa Allah

"Na yi nadamar abin da na aikata kuma a shirye na ke in sauya rayuwa ta. A shirye na ke in fara bawa matata da yara na kudin abinci."

Alkaliyar kotun, Mrs S.M. Akintayo ta dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 1 ga watan Maris domin yanke hukunci, ta kuma shawarci ma'auratan su tabbatar sun cigaba da zaman lafiya.

Kare ya fi ni daraja a idon mijina, Mata ta nemi alkali ya raba aurenta

A wani labarin daban, wata mata mai suna Rashidat Ogunniyi ta bayyana gaban kotu inda ta yi wa alkali korafi akan yadda mijinta ya fi son karenta akan ta, Premium Times ta ruwaito.

‘Yar kasuwar mai shekaru 40 ta bukaci alkali ya warware igiyar aurensu mai shekaru 12 inda ta sanar da yadda hankalin mijinta ya fi karkata akan karensa.

Kamar yadda ta ce:

“Kazeem ba miji ko kuma uba na gari bane, ba ya nuna min so balle kuma yaransa. “Damuwarsa kadai akan karensa ta ke. Ya na nuna wa karensa so da kauna kwarai.”

Kara karanta wannan

Gombe: Mai adaidaita sahu ya yi garkuwa da kansa don ya samu N500,000 ya biya bashin da 'yar uwarsa ke binsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel