Matashi ya shiga hannu yayin da yake kokarin tserewa bayan fille kan budurwarsa

Matashi ya shiga hannu yayin da yake kokarin tserewa bayan fille kan budurwarsa

  • Yan sanda a jihar Ogun yi nasarar damke wani matashi mai shekaru 18, Soliu Majekodunmi wanda ya tsere bayan fille kan budurwarsa
  • Saurayin ya hada kai da wasu abokansa su uku wajen yanke kan budurwar domin yin kudin asiri
  • Asirinsu ya tonu ne a lokacin da suke kona kokon kan a cikin wata tukunyar kasa

Ogun - Rundunar yan sandan jihar Ogun ta kama wani matashi mai suna, Soliu Majekodunmi da ya tsere bayan ya jagoranci kashe budurwarsa.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, a wani karin haske da yayi kan kisan yarinyar mai suna Rofia da wasu matasa hudu suka yi a Abeokuta, ya ce an kama jagoran kungiyar, jaridar Punch ta rahoto.

Oyeyemi ya tabbatar da cewar matasan su hudu sun yanka da kuma kona kokon kan Rofia bayan saurayinta, Soliu ya yaudareta zuwa gidansa a Oke-Aregna.

Kara karanta wannan

Bakar wahala: Fasto ya hango irin bala'in da 'yan Najeriya za su shiga a 2022

Matashi ya shiga hannu yayin da yake kokarin tserewa bayan fille kan budurwarsa
Matashi ya shiga hannu yayin da yake kokarin tserewa bayan fille kan budurwarsa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa an kama matasan wadanda shekarunsu ke tsakanin 17 da 20 a safiyar Asabar, 29 ga watan Janairu kan zargin kashe budurwar abokinsu don kudin asiri.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai gadin garin, wani Segun Adewusi ya ce sun lura cewa wasu yara na kona wani abu a tukunyar kasa.

Nan take sai mai gadin ya sanar da ofishin yan sandan Adatan, wadanda suka je wajen sannan suka kama yaran uku yayin da Soliu, jagoransu ya tsere kafin zuwan yan sandan.

Yarinyar da aka kashe ta kasance mazauniyar Idi-Ape Abeokuta kuma budurwar Soliu, wanda a yanzu yake a hannun yan sanda.

Yadda aka kama Soliu

Da yake bayanin yadda aka kama Soliu, kakakin yan sandan ya ce an ba DPO umurnin kamo shi.

Ya ce:

"Bayan samun umurnin kwamishinan yan sanda na tabbatar da kamun saurayin marigayiyar, sai DPO na Adatan da jami'ansa suka shiga aiki inda suka kamo wanda ake zargin Soliu Majekodumi a mabuyarsa. Shekararsa 18."

Kara karanta wannan

2023: Zan kawar da karuwai idan nayi nasara a zabe, Dan takaran shugaban kasa yayi alkawari

An ce Soliu ya yaudari yarinyar zuwa dakinsa, inda ya danneta sannan ya nemi daya daga cikin abokansa ya yanka ta da wuka.

Sauran wadanda aka kama tun da farko sune; Wariz Oladeinde mai shekaru 17 daga Kugba, Abdulgafar Lukman mai shekaru 19 daga Kugba da Mustakeem Balogun daga Bode Olude, duk a Abeokuta.

Rundunar ‘yan sandan ta ce:

“Sun kashe Rofiat ne, suka yanke mata kai, suka tattara gawar mara kai a cikin buhu sannan suka fara kona kan a tukunya. Sun gaya wa ’yan sanda a gaban taron jama’a cewa suna so su yi amfani da shi don yin kudin asiri ne.”

Duniya kenan: Matashi mai shekaru 35 ya kashe mahaifiyarsa, ya gamu da fushin alkali

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata kotun majistare da ke Ado Ekiti ta amince da bukatar da aka gabatar gabanta na ci gaba da tsare wani dan shekaru 35 mai suna Abiola Ayodeji a gidan gyara hali, Ado Ekiti.

Kara karanta wannan

Iyayen mutumin da ya kashe Hanifa sun gudu daga gidansu saboda tsoron hari

Dan sanda mai gabatar da kara, Bankole Olasunkanmi ne ya bukaci hakan, domin ba rundunar yan sanda damar kammala bincike.

Ana zargin Abiola da kashe mahaifiyarsa mai shekaru 75, Abiola Olaitan Florence, a ranar 11 ga watan Janairu a unguwar Ipole-Iloro a Jihar Ekiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel