Bakar wahala: Fasto ya hango irin bala'in da 'yan Najeriya za su shiga a 2022

Bakar wahala: Fasto ya hango irin bala'in da 'yan Najeriya za su shiga a 2022

  • Babban faston nan na Najeriya, Prophet Wale Olagunju, ya yi hasashen abubuwan da za su faru a kasar a 2022
  • Faston ya ce yan Najeriya za su kara tsintar kansu a bakar wahala a wannan shekarar
  • Ya kuma bayyana wasu tarin kalubale da yan siyasar kasar za su fuskanta a 2023, inda ya ce manyan yan Najeriya da dama za su mutu

Wani babban faston Najeriya, Prophet Wale Olagunju ya bayyana manyan abubuwan da za su tunkaro kasar na neman ballewa a hasashensa na 2022, inda ya yi kira ga masu neman ballewa da su jira hukuncin Allah idan har suna son cimma burinsu.

Jaridar The Sun ta rahoto cewa malamin addinin mazaunin Ibadan, wanda ke jagorantar cocin Divine Seed of God Chapel Ministries, Ojoo, ya ce yan Najeriya za su fuskanci karin wahala a shekarar 2022.

Kara karanta wannan

2023: Matasan arewa sun roƙi Ɗangote da Otedola su fito takarar shugabancin ƙasa

Bakar wahala: Fasto ya hanya irin bala'in da 'yan Najeriya za su shiga a 2022
Bakar wahala: Fasto ya hanya irin bala'in da 'yan Najeriya za su shiga a 2022 Hoto: Divine Seed Ministry
Asali: Facebook

A hasashen da ya saki a yayin bauta a coci, faston ya ambaci jerin sunayen mutanen da ya bayyana a matsayin shugabannin da suka garkame Najeriya sannan cewa dole wadannan mutane su bar matakin a matsayin hanyar farko na raba kasar.

Faston ya kuma bayyana irin kalubalen da ke gaban wasu manyan yan siyasa da jam'iyyun siyasa yayin da kasar ke shirye-shiryen babban zabe a 2023.

Prophet Olagunju ya ce:

"Allah ya ce wahalar rayuwa za ta ci gaba a Najeriya yayin da Buhari zai jawo wahalhalu. Don haka, yan Najeriya na bukatar kai kukansu ga Allah domin ya shiga lamarin.
"Allah ya ce manyan yan Najeriya da dama za su mutu a shekarar 2023.
“Allah ya ce za a samu tashin hankali a kasar nan a 2022. Allah ya ce jinin ‘yan Najeriya da aka zubar suna kuka a kunnuwansa domin daukar fansa.

Kara karanta wannan

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

“Ya kamata ‘yan Najeriya su yi addu’a sosai kan hadarin jirgin."

Game da zaben 2023, The Sun ta nakalto faston yana cewa:

"Allah ya ce Atiku Abubakar zai shahara sosai a zaben shugaban kasa na 2023 a Najeriya a arewa fiye da sauran yankunan kasar. A bisa ga abun da aka nuna mun, a zaben 2023, sunan Atiku zai yi amo kamar kararrawa.
"Koda jam'iyya mai mulki a kasar ta baiwa babban jigonta na kasa, Sanata Bola Tinubu tikitin takarar shugaban kasa, ba shi Allah ya zaba don ya mulki kasar ba.
"Allah ya ce idan APC ta bai wa Tinubu tikitinta a babban zaben 2023, arewa ta dana wa nutanen kudu tarko don tabbatar da faduwarsa.
"Yawancin mambobin jam'iyya mai mulki a kasar za su sauya sheka zuwa PDP gabannin zaben shugaban kasa na 2023 kuma wannan zai ba PDP damar nasara a zaben shugaban kasa."

Sauya sheka: Yari da Marafa sun gana da Atiku da Saraki

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Malaman makarantun firamare a Abuja sun tsunduma yajin aiki

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari, ya yi wata ganawa tare da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a ranar Alhamis, 27 ga watan Janairu.

Hakazalika Sanata Kabiru Marawan wanda ya wakilci Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawa ta takwas ma ya kasance a cikin ganawar, The Nation ta rahoto.

A yanzu haka, Yari da Marafa suna wakiltan tsagi biyu mabanbanta a jam'iyyar APC reshen Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel