Da dumi-dumi: Jami’in dan sanda ya bindige matashi kan ya sha ‘pure water’ ba tare da izininsa ba

Da dumi-dumi: Jami’in dan sanda ya bindige matashi kan ya sha ‘pure water’ ba tare da izininsa ba

  • Wani jami'in dan sanda ya bindige wani matashi bayan sabani ya shiga tsakaninsu a garin Kabba da ke karamar hukumar Kabba/Buni na jihar Kogi
  • Matashin ya dauki ruwan 'pure water' daga motar dan sandan don ya sha ba tare da ya bashi izini ba, hakan sai ya tunzura jami'in tsaron
  • Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar al'amarin a ranar Asabar, 22 ga watan Janairu

Kogi - Wani jami’in dan sanda ya harbe wani matashi bayan rigima ta kaure tsakaninsu kan ruwan leda wato 'pure water' a garin Kabba da ke karamar hukumar Kabba/Buni na jihar Kogi a safiyar Asabar, 22 ga watan Janairu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa faruwan hakan ya haifar da gagarumin zanga-zanga a garin, lamarin da ya tsayar da harkokin kasuwanci cak.

Kara karanta wannan

Ruwan Wuta: Yan sanda sun yi magana kan jihar da Bello Turji ya koma bayan tserewa daga Zamfara

Wani idon shaida ya ce yaron ya dauki ruwan leda daga motar dan sandan domin ya sha ba tare da izininsa ba.

Da dumi-dumi: Jami’in dan sanda ya bindige matashi kan ya sha ‘pure water’ ba tare da izininsa ba
Da dumi-dumi: Jami’in dan sanda ya bindige matashi kan ya sha ‘pure water’ ba tare da izininsa ba Hoto: KOLA SULAIMON / AFP
Asali: Facebook

An tattaro cewa abun da yaron ya aikata ya tunzura jami’in dan sandan inda ya harba kunamar bindigarsa ga yaron kuma ya kashe shi a nan take.

Ya kare kansa ne - Hukumar yan sanda

A martaninsa, kwamishinan yan sandan jihar Kogi, CP Edward Egbuka, ya bayyana cewa bayanai daga kwamandan yan sandan yankin ya banbanta da ikirarin da ake yayatawa.

CP Egbuka ya kara da cewa dan sandan ya yi kokarin kare kansa daga matashin ne, inda yayi alkawarin gudanar da bincike kan lamarin da kuma gano gaskiyar lamura.

Yayin da yake tabbatar da kisan, CP din ya ce za a san gaskiyar ne bayan bincike.

Kara karanta wannan

Mutum daya ya mutu sakamakon gardama kan Chelsea da Barcelona a Katsina

Daily Trust ta tattaro cewa Jami’an yan sanda a Kabba na kokarin kwantar da hatsaniyar da ya faru a garin sakamkon lamarin.

Yan bindiga na kwantawa da matanmu da yayanmu mata saboda rashin biyan harajin N2m – Mazauna Zamfara

A wani labari na daban, mazauna garuruwa biyar da ke karkashin yankin Kurya Madaro a karamar hukumar Kaura Namoda da ke jihar Zamfara sun tsere daga gidajensu bayan yan bindiga sun koma yiwa matansu da yayansu mata fyade saboda rashin biyan kudin harajin da suka daura masu.

An tattaro cewa mazauna garuruwan da abun ya shafa sun zabi tserewa don tsira daga ci gaban hare-hare bayan sun gaza biyan yan bindiga naira miliyan 2 da suka daurawa kowannensu.

A wata hira da jaridar Tribune, wani mazaunin Balankadi, Malam Rabi'u Abubakar, wanda ke samun mafaka a wajen garin, ya ce yan bindigar sun ce lallai sai sun biya naira miliyan 2 kafin su barsu su samu zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Kamar wasa: Yadda matashi ya sayar da hotunansa na selfie kan kudi N415m

Asali: Legit.ng

Online view pixel