'Karancin man fetur: Za mu yi zanga-zanga, N200 muke siyan lita, Mutanen garin Saki

'Karancin man fetur: Za mu yi zanga-zanga, N200 muke siyan lita, Mutanen garin Saki

  • Mutanen garin Saki da ke Jihar Oyo sun koka kan karancin man fetur wanda hakan yasa aka fara sayar da lita kan N200
  • Mazauna garin sun ce a halin yanzu kwata-kwata babu gidan mai a garin da ke sayar da fetur, suna zargin ana karkatar da man zuwa Jamhuriyar Benin
  • Mutanen garin sun yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin da abin ya rataya a kansu su dauki mataki idan ba haka ba za su yi zanga-zanga

Jihar Oyo - Mazauna garin saki da ke yankin Oke-Ogun na Jihar Oyo, a ranar Alhamis sun yi barazanar yin zanga-zanga kan karancin man fetur tare da karin farashin man fetur da aka fi sani da PMS, Daily Trust ta ruwaito.

Sun bayyana cewa babban dalilin da ya janyo karancin man fetur din shine karkatar da man da ake yi zuwa Jamhuriyar Benin inda suka shawarci gwamnati ta dauki matakin magance lamarin.

Kara karanta wannan

Samun man fetur ya yi wahala, jama'a sun koka, sun ce za su fara zanga-zanga

Karancin man fetur: Mazauna Saki sun yi barazanar yin zanga-zanga, ana sayar da lita N200
Mazauna Saki sun koka kan karancin man fetur, ana sayar musu da lita kan N200. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Saki wani gari ne da ke kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mr Lawal Kunle, shugaban kungiyar cigaban mutanen Saki, Saki First, ya tabbatar da karancin na man fetur ga wakilin Daily Trust a Ibadan ya ce lamarin ya shafi dukkan kasuwanci a yankin.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta saka ido kan masu kasuwancin man fetur a yankin domin tabbatar da cewa ba su kuntata wa rayuwar mutanen Saki ba.

Martanin wasu mazauna Saki

Wani mazaunin garin Saki da ya nemi a boye sunansa ya ce dillalan man fetur da dama suna karkatar da man fetur din zuwa wasu kasashe yayin da mutanen garin suke wahala.

Ya ce:

"Idan farashin man fetur ya karu ne amma za mu same shi cikin sauki, ba mu da matsala da hakan amma matsalar shine ba mu samun shi cikin sauki. A yanzu da muke magana, babu gidan mai da ke sayar da fetur yanzu a Saki.

Kara karanta wannan

Idan kuka kara farashin mai, zaku sake jefa miliyoyin mutane talauci: Janar AbdulSalam

"Hakan yasa masu acaba sun ninka kudin da suke karba. Ko pure water ma N15 ake sayarwa. Kowa na cewa karancin man ne ya janyo tsadar. Ba za mu iya cigaba a haka ba."

An yi kokarin ji ta bakin hukumar kula da albarkatun man fetur, DPR, na jihar amma hakan ya ci tura domin kakakin hukumar, Niyi Olowokekere, ya kashe wayansa kuma bai amsa sakon text ba.

Kungiyar Kirista Ta Najeriya Ta Buƙaci Buhari Ya Janye Tallafin Man Fetur Kafin 2023

A wani labarin, kun ji cewa Kungiyar Kirista ta Najeriya, NCF, gammayar mabiya Katolika da Protestant ta ce ya zama dole gwamnatin tarayyar Najeriya ta jajirce ta ceto kasar daga rushewa ta hanyar cire tallafin man fetur, .

NCF ta ce akwai alamu kwarara da ke nuna cewa idan an cire tallafin man fetur, da aka ce yana lashe kimanin Naira biliyan 250 duk wata, tattalin arzikin zai shiga mummunan hali, Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An dakatar da dagaci kan yi wa budurwa auren dole, cin zarafin mahaifin ta da nada mata duka

A wani taron manema labarai a Abuja, shugaban NCF, Bishop John Matthew, tare da sauran shugabannin kungiyar, sun ce tallafin man fetur babban kallubale ne da ya kamata a tunkare shi gadan-gadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel