Da duminsa: EFCC ta titsiye Supo Shasore, tsohon kwamishinan Legas kan damfarar P&ID

Da duminsa: EFCC ta titsiye Supo Shasore, tsohon kwamishinan Legas kan damfarar P&ID

  • Jami'an hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta titsiye Olasupo Shasore
  • Tabbatacciyar majiya daga EFCC ta ce an fara tuhumar tsohon kwamishinan jihar Legas din ranar Talata bayan ya kai kan sa hukumar
  • An gano cewa, ana tuhumar antoni janar din kuma babban lauyan ne kan rawar da ya taka a damfarar P&ID

Jami'an hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC a halin yanzu sun titsiye tsohon antoni janar kuma kwamishinan shari'a na jihar Legas, Olasupo Shasore, (SAN).

Wata majiya tabbatacciya daga hukumar ta sanar da Daily Trust cewa, babban lauyan ya halarci hedkwatar hukumar a ranar Talata.

Da duminsa: EFCC ta titsiye Supo Shasore, tsohon kwamishinan Legas kan damfarar P&ID
Da duminsa: EFCC ta titsiye Supo Shasore, tsohon kwamishinan Legas kan damfarar P&ID. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Majiyar ta ce ana tuhumar sa ne kan rawar da ya taka a damfarar aikin Process & Industrial Development.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mutane sun shiga daji sun kwato Sarkin su da yan bindiga suka sace a Filato

Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya dauka alkawarin sanar da abinda ke faruwa bayan da aka tuntube shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel