Mawaki ya yi tsokaci kan budurwar da ta rude, ta na neman zabi tsakanin saurayi da kuma karatu kasar waje

Mawaki ya yi tsokaci kan budurwar da ta rude, ta na neman zabi tsakanin saurayi da kuma karatu kasar waje

  • Wata budurwa ta shiga rudani yayin da ta nemi a bata shawara kan wanda za ta zaba tsakanin saurayinta da kuma tallafin karatu kyauta a kasar waje
  • Budurwar ta shiga tsaka mai wuyo domin saurayin nata ya yi barazanar rabuwa da ita idan ta tafi karatun
  • Shahararren mawaki Ric Hassani ya shawarta da tayi fatali da batun wani saurayi sannan ta rungumi karatunta

Shahararren mawakin nan na Najeriya, Ric Hassani, ya yi martani ga budurwar da ke tunanin wanda za ta zaba tsakanin saurayinta da kuma tallafin da ta samu na yin karatu a kasar waje.

A ranar Asabar ne Rita Orji, wata yar Najeriya mai bincike da ke zama a Canada, ta je shafinta na Twitter domin bayyana wani sako da ta samu a akwatin sakonta na gmail daga wata budurwa mai shekaru 22.

Kara karanta wannan

Tiwa Savage: Na so ace Dangote mahaifi na ne, amma kash

Ric Hassani ya yi tsokaci kan budurwar da ta rude, ta na neman zabi tsakanin saurayi da kuma karatu kasar waje
Ric Hassani ya yi tsokaci kan budurwar da ta rude, ta na neman zabi tsakanin saurayi da kuma karatu kasar waje Hoto: MediaNews Group/Long Beach Press-Teleg and Neustockimages
Asali: Getty Images

A cewar Orji, budurwar ta samu tallafi kwanan nan domin tafiya yin digir na biyu a kasar waje.

Sai dai kuma, ta ce budurwar ta shiga tsaka mai wuya yayin da saurayinta yayi barazanar rabuwa da ita idan har ta tafi waje yin karatun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarta, budurwar tana tsoron rasa saurayin nata domin ya yi alkawarin aurenta.

Orji ta ce budurwar ta aike mata wasikar ne domin jin ra'ayinta da na sauran mutane game da abun yi.

Ta rubuta a shafinta:

"Na wayi gari da sakon email din wata budurwa da ta samu gurbin yin karatun digiri na biyu a kasar waje kyauta saurayinta ya fada mata ta zaba tsakanin karatun da ita. Tana neman shawara."

Wallafan ya janyo cece-kuce daga yan Najeriya da dama, inda wasu ke amfani da maudu'in ‘#She’s22.

Da yake martani kan lamarin, Hassani ya bukaci budurwar da ta zabi tallafin karatu da ta samu sama da saurayinta.

Kara karanta wannan

Matar aure ta tsere da saurayinta ta bar mijinta da suka shafe shekaru 3 tare

Mawakin ya yi alkawarin halartan auren matashiyar idan ta kammala karatunta sannan ta samu mijin da yake nata.

"A shekaru 22, idan kina karanta wannan, dan Allah kyale wannan saurayin, toshe shi a dukka dandamali, je ki yi digirinki na biyu sannan ki karu kamar yadda Allah ya nufa. Zan yi waka a wajen bikinki idan kika hadu da mutumin da ya dace da ke. Ina fatan za ki ga wannan."

Legit Hausa ta kuma ji ra'ayoyin wasu mutane game da wannan lamari.

Da aka nemi jin ta bakinta, wata budurwa mai suna Humaira ta ce:

"Ai ni ko, idan ni ce budurwar, ba zan ma yi shawara ba, abu mai sauki ne, karatu na zan tafi. Babu wani tsayawa shawara tsakanin saurayi da karatu."

Hakazalika wani mutum da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce:

"Ilimi dai ci gaban dan Adam ne, kuma bai da ce ya hana ta zuwa karatu ba matukar yana son ci gaban ta. Sannan, ai bai aure ta ba, idan ya yanke shawarar fasa ci gaba da alaka da ita ya kenan?

Kara karanta wannan

Tana wasa da lafiyarta: Bidiyon yadda wata mata mai ciki ta zaƙe wurin kwasar rawa da ƙarfinta na bara

"Ba ta tsuntsu bata da tarko kenan. Saboda haka, ta yi watsi da maganarsa ta kama karatu, Allah zai ba ta mai son ci gabanta."

Iyayen zamani: Iyaye sun sa dansu a gaba da fada saboda ya ki kawo budurwa gida

A gefe guda, anji wata uwa da uba a Najeriya suna koka damuwa matuka cewa dan su bai kawo yarinya gidansu ba tsawon shekaru takwas da suka gabata. Sun tuna a wani faifan bidiyo cewa ba a ga dan da wata yarinya ba tsawon yadda za a iya tunawa.

A wani faifan bidiyo da @instablog9ja ya wallafa a Instagram, an ga dan yana zaune dirsham yana jin iyayensa cikin nutsuwa. Mahaifiyar ce ke magana yayin da uban ya amince da wasu 'yan kalamanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel