Hotuna da bidiyon motar N460 miliyan da Dino Melaye ya siya

Hotuna da bidiyon motar N460 miliyan da Dino Melaye ya siya

- Tsohon sanatan Najeriya mai wakiltar Kogi ta yamma, ya bayyana sabuwar motar da siya ta alfarma

- Sanata Dino Melaye ya siya motar alfarma kirar Lamborghini Aventador Roadstar wacce darajarta ta kai dala miliyan daya

- Wani fitacce a kafafen sada zumuntar zamani, tundeednut ne ya wallafa hotuna da bidiyon motar a Instagram

Dino Melaye, tsohon sanata da ya taba wakiltar yankin Kogi na yamma, ya darzo sabuwar motar kirar Lamborghini Aventador Roadstar.

Tunde Ednut ne ya wallafa hotuna tare da bidiyon motar alfarmar a shafinsa a ranar Asabar da ta gabata.

Fitaccen sananne a shafukan sada zumuntar ya wallafa hoton tsohon dan majalisar yana tuka motarsa mai darajar dala miliyan daya wanda yayi daidai da N460,000,000.

"Sanata Dino Melaye ya siya sabuwar mota kirar Lamborghini Aventandor Roadstar kirar 2020. Kamfanin sun fitar da ita ne a bikin cikarsu shekaru 50. Wannan tana daya daga cikin guda 100 da kamfanin suka yi su a kan dala miliyan 1," ya wallafa a Instagram.

A watan Maris da ya gabata, tsohon sanatan ya koka da tarin dawainiyar da ke kansa duk da hotunan katafaren gidansa da ya wallafa nasa a kasar ketare.

"Ku taya ni dauka, ku taya ni dauka. Dawainiyar da ke kaina suna karuwa, bakina yana kara fadi," Melaye yace a harshen Yarabanci.

KU KARANTA: Buhari ya tabbatar da tabarbarewar tattalin arziki da tsaro a Najeriya

Hotuna da bidiyon motar N460 miliyan da Dino Melaye ya siya
Hotuna da bidiyon motar N460 miliyan da Dino Melaye ya siya. Hoto daga tundeednut
Asali: Instagram

KU KARANTA: Nigeria @ 60: Ministan Buhari ya tabbatar da cewa ba zai yuwu a raba Najeriya ba

A wani labari na daban, hotuna da bidiyon katafaren gidan Dino Melaye da tsadaddun kayayyakinsa sun bayyana a yanar gizo.

Wani babban dan jarida kuma dan kasuwa, Dele Momodu ne ya wallafa bidiyon a lokacin da ya kai ziyara tare da zagawa lungu da sako na gidan.

An gano Dino yana kewayawa da Momodu a gidan nasa mai kama da aljannar duniya da ke Abuja, inda ya nuna masa tsadaddun agogunan hannu, takalma, turarruruka, motoci, madafi, wajen cin abinci da sauransu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel