Innalillahi: 'Yan bindiga sun kutsa gidaje a Zamfara, sun hallaka wani basarake

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kutsa gidaje a Zamfara, sun hallaka wani basarake

Zamfara - An harbe wani hakimi mai suna Alhaji Umaru Bawan Allah a wani hari da aka kai a unguwar Gada dake karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Daily Trust ta tattaro cewa an kashe wasu mutane biyar a harin wanda ya faru da sanyin safiyar ranar Laraba.

'Yan ta'adda sun aikata barna a Zamfara
Innalillahi: 'Yan bindiga sun kutsa gidaje a Zamfara, sun hallaka sarkin gargajiya | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Mazauna yankin sun ce wasu ‘yan bindiga da dama ne suka afkawa al’ummar garin da misalin karfe daya na dare, inda suka shiga gida-gida, suka sace mutane kana suka harbe wasu har lahira.

'Yan ta'addan sun kuma yi awon gaba da wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba, da suka hada da mata da kananan yara, wadanda akasarinsu aka kama a lokacin da suke kokarin tserewa.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Duk da haka, tare da hadin gwiwar 'yan banga na yankin da jami'an tsaro an ceto mutanen da aka sace."
“An gano 'yan bindigan ne a wani wuri kusa da yankin Karakkai. Jami’an tsaro sun taru inda ‘yan banga na yankin suka taimaka wajen tare hanyar.
"Bayan wani mummunan artabu, 'yan bindigar sun yi bar wadanda aka sace, watakila saboda ba su da yawa."

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel