Yan bindiga sun kashe dan Bijilanti, sun yi awon gaba da DSS a Abuja

Yan bindiga sun kashe dan Bijilanti, sun yi awon gaba da DSS a Abuja

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun sace jami'in hukumar yan sanda ta farin kaya (DSS) a babban birnin tarayya Abuja
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun kashe wani jami'in sa'kai ɗan bijilanti guda ɗaya yayin harin na ranar Asabar da daddare
  • Rundunar yan sandan Abuja ta bakin kakakinta tace sam ba ta samu bayanai game da kai harin da sace jami'in ba

Abuja - Wasu yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace jami'in hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) yayin wani hari kan mutanen yankin Abaji, dake Abuja ranar Asabar.

Punch ta rahoto cewa yan bindigan sun kuma hallaka wani ɗan bijilanti yayin harin wanda ya suka kai da tsakar dare.

Yan bindigan sun shiga yankin ne da adadi mai yawa da mutanen su, kuma kai tsaye suka farmaki ofishin jami'an DSS dake yankin.

Kara karanta wannan

Nasara: Sojoji sun ragargaji sansanin dan bindiga Bello Turji, sun hallaka da dama

Yan bindiga
Yan bindiga sun kashe dan Bijilanti, sun yi awon gaba da DSS a Abuja Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sai dai har yanzun da muke haɗa wannan rahoton, babu tabbacin ko maharan sun tuntubi iyalan jami'in kan kudin fansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sanda reshen babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, tace ba ta da masaniya kan abinda ya faru, kuma ta bukaci manema labari su nemi karin bayani a wurin DSS.

A nasu bangaren, kakakin jami'an DSS, Peter Afunanya, bai ɗaga kiran wayan da aka masa ba domin neman ƙarin bayani.

Yankin Abaji a babban birnin tarayya Abuja ya zama wani sanannen wuri da yan ta'adda ke cin karen su babu babbaka.

Daga cikin ayyukan ta'addancin da ake yawan aikata wa a Abaji akwai satar mutanen yankin da kuma matafiya akan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja domin neman kudin fansa.

A wani labarin na daban kuma Jami'an kwastam sun damke babbar kwantena maƙare da bindigu a Legas

Kara karanta wannan

Dubun yan bindigan da suka kashe mutane a masallaci a jihar Neja ya cika

Yayin da lamarin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a Najeriya, jami'an kwastam sun yi babban nasarar dakile yunkurin shigo da makamai.

Jami'an kwastam na Tin Can a Legas sun yi ram da wata kwantema makare da katan-katan na bindigu da harsasai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel