Hukumar Kwastam ta yi ram da kwantena cike da bindigogi da harsasai a Tin Can Legas

Hukumar Kwastam ta yi ram da kwantena cike da bindigogi da harsasai a Tin Can Legas

Tin Can, Lagos - Jami’an Hukumar hana fasa kwabri watau Kwastam a ranar Juma’a 17 ga Disamba 2021 sun cika hannu kwantena jigbe da bindigogi da harsasai a tashar Tin Can Legas.

Mai kwantenan ya yo ikirarin cewa kayan wuta ke ciki amma yayinda jami’an Kwastam suka bude, sai suka ci karo da bindigogi katon-katon, Punch ta ruwaito.

Kakakin hukumar Kwastam na Tin Can, Uche Ejesieme, ya tabbatar da hakan ranar Asabar, 18 ga Disamba, The Nation ta kara.

Ejieseme ya kara da cewa za’a sake lalube dukkan abubuwan dake cikin kwantenan daga baya kuma a sanar da al’umma abin da aka gani.

Hukumar Kwastam ta yi ram da kwantena cike da bindigogi da harsasai a Tin Can Legas
Hukumar Kwastam ta yi ram da kwantena cike da bindigogi da harsasai a Tin Can Legas

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Online view pixel