Yanzu-Yanzu: Bayan Na Kaduna, Wani Ɗan Majalisar Da Ƴan Bindiga Suka Harba Ya Mutu

Yanzu-Yanzu: Bayan Na Kaduna, Wani Ɗan Majalisar Da Ƴan Bindiga Suka Harba Ya Mutu

  • Honourable Jude Adjekpovu mai wakiltar Ethiope-East ta jihar Delta ya rasu a safiyar yau Alhamis a wani asibiti mai zaman kansa bayan jinya na kimanin mako daya
  • Wasu da ake kyautata zaton 'yan bindige ne suka harbe Adjekpovu a ranar 4 ga watan Disamba a hanyarsa ta dawowa daga wani taro a Eku/Abraka
  • Wata majiya daga unguwar su kansilar ta tabbatar da rasuwarsa sai da rundunar yan sandan jihar Delta ta bakin kakakinta Bright Edafe ta ce bata san da batun ba

Delta - Kansilar karamar hukumar Ethiope-East a jihar Delta, Honourable Jude Adjekpovu ya mutu sakamakon raunin da ya yi bayan da wasu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne suka harbe shi da bindiga, SaharaReporters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An bukaci hukumar EFCC ta binciki dukiyar jagoran APC, Bola Tinubu da Akande

Hakan na zuwa ne mako guda bayan wasu da aka ce yan bindiga ne sun harbi Adjekpovu a hanyar Eku/Abraka a karamar hukumar Ethiope-East ta jihar Delta a lokacin da ya ke dawowa daga wani taro.

Yanzu-Yanzu: Bayan Na Kaduna, Wani Ɗan Majalisar Da Ƴan Bindiga Suka Harba Ya Mutu
Dan majalisa da yan bindiga suke harbe a Delta ya rasu bayan jinya. Hoto: LIB
Asali: Facebook

SaharaReporters ta gano cewa dan majalisar ya rasu ne a ranar Alhamis da safe a wani asibiti mai zaman kansa inda ake masa magani tun ranar Asabar 4 ga watan Disamba bayan an harbe shi.

Majiya daga unguwar dan majalisar ta tabbatar da mutuwarsa

Wata majiya daga yankin dan siyasan ta ce:

"Ya rasu a ranar Alhamis da safe bayan ya shafe a kalla mako guda yana jinya."

Kansilar na karamar hukuma wanda ke wakiltar mazaba ta 5 a karamar hukumar Ethiope East ya shafe kimanin mako guda yana jinya bayan harbin da 'yan bindigan suka masa.

Kara karanta wannan

Dubun yan bindigan da suka kashe mutane a masallaci a jihar Neja ya cika

Yan bindigan da ake zargi makiyaya ne sun tare hanyar Eku-Abraka misalin karfe 5.30 na yamma a ranar suka kuma bude wa motar kansilar wuta.

An ruwaito cewa harsashi ya ratsa cikinsa.

Amma a yayin da SharaReporters ta tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya ce ba shi da masaniya a kan afkuwar lamarin.

'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto

A wani labarin, 'yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a a jam'i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai.

Kara karanta wannan

Yanzu kam lokaci ya yi da ya kamata kowa ya nemi makami, gwamna Masari ya magantu

Asali: Legit.ng

Online view pixel