Bayan barranta da 'yan bindiga, Gumi ya tura sako ga masu cewa ya kamata a kama shi

Bayan barranta da 'yan bindiga, Gumi ya tura sako ga masu cewa ya kamata a kama shi

  • Sheikh Ahmadu Gumi ya mayar da martani ga masu kira da a kama shi kan alakarsa da ‘yan bindiga da ke addabar Arewa
  • Malam Gumi, mazaunin Kaduna, ya ce masu neman jami’an tsaro su kama shi, ba su da bambanci da ‘yan bindiga
  • Malamin ya kara da cewa, munafunci ne a ce yana goyon bayan ‘yan ta’adda ko kuma daukar nauyin ‘yan ta’adda, yana mai cewa shi yana kokarin hana ta'addanci ne

Kaduna – Shahararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana masu kira da a kamo shi kan alaka da ‘yan bindiga da ke addabar yankin Arewacin Najeriya a matsayin wawaye.

Gumi dai duk da bacin ran da jama’a suke nunawa, ya sha ganawa da wasu ‘yan bindiga inda ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi musu afuwa kamar yadda ta yi wa tsagerun Neja Delta.

Kara karanta wannan

Matar da tace tana kallo 'yan bindiga suka kona mahaifiyarta da 'ya'ya 4 ta rasu

Malamin addinin Islama
Bayan barranta da 'yan bindiga, Gumi ya tura sako ga masu cewa ya kamata a kama shi | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Facebook

Sai dai ‘yan Najeriya da dama sun yi kira da a damke malamin da ke zaune a Kaduna, inda suka zarge shi da daukar nauyin ‘yan bindigar da kuma tallafa musu.

Da yake mayar da martani kan kiran da ake yi na kama shi a wata hira da ya yi da Premium Times, Sheikh Gumi ya ce:

"Su wawaye ne, ba su san komai game da al'ummar Najeriya ba, ba su san tsarin mulkin Najeriya da 'yanci ba, hakkin tsarin mulki ne mutum ya bayyana ra'ayinsa, don haka ba za ku yi kira da a kawo tashin hankali ba ko a ce cutar da wani.
“Wadannan mutanen da suke kira a kama ni, ban gan bambancinsu da ‘yan bindigan ba, a ce wai ina goyon bayan ‘yan bindiga ko kuma daukar nauyin ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Bayan Ƙona Fasinjoji Da Ransu, Ƴan Bindiga Sun Sake Zubar Da Jini a Wani Gari a Sokoto

"Ina kokarin warkar da su ne ta hanya ta, ina kokari na hana su ta hanya ta kuma na ga yadda karamin kokarina ya taimaka. Ina da ra'ayi ne daban na magance matsalar. Amma don karfafa musu? A'a. Don a taimake su? A'a, ba zai yuwu ba, ni ma ina fama da illar 'yan bindiga."

Sheikh Gumi ya ce ba ruwansa da 'yan bindiga yanzu kam, ya fadi dalili

A tun farko, shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce ya daina shiga don sasantawa da ‘yan bindiga biyo bayan ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda da kotu ta yi.

Premium Times ta ruwaito cewa Gumi ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman a Kaduna a ranar Laraba 8 ga watan Disamba.

Kafin babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ayyana 'yan bindigan a matsayin ‘yan ta’adda, Gumi ya sha ziyartarsu a dazuzzukan jihohin Zamfara da Neja.

Kara karanta wannan

Harin Sokoto: Ina kallo 'yan bindiga suka kona mahaifiya ta da 'ya'ya na 4 da ransu, Shafa'atu

Asali: Legit.ng

Online view pixel