Ba a sace matafiya a Maiduguri ba: Rundunar soji ta bayyana abin da ya faru

Ba a sace matafiya a Maiduguri ba: Rundunar soji ta bayyana abin da ya faru

  • Rundunar sojin Najeriya ta bayyana yadda wasu kafafen sada zumunta ke yada labaran karya kan sace matafiya a Borno
  • Rundunar ta ce ba a sace wasu matafiya a Maiduguri ba, don haka ya kamata mutane su guje wa yada jita-jita
  • Hakazalika, rundunar ta bayyana gaskiya abinda ya faru, inda tace kuma tuni ta magance matsalar da ta kunno

Borno - A jiya Asabar ne rundunar sojin Najeriya ta karyata rahotannin jita-jita da ke yawo a kafafen sanda zumunta na sace matafiya a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a ranar 11 ga watan Disamba.

Ado Isa, wani jami'in soji, wanda shi ne mai magana da yawun runduna ta 7 ta Operation Hadin Kai, ya ce wannan jita-jita ba ta da tushe ko asali.

A makon da ya gabata ne a aka samu rahotannin da ke bayyana cewa, 'yan ta'adda a Arewa masi gabashin Najeriya sun sace wasu matafiya a yankin Maiduguri.

Kara karanta wannan

Dala daya (N409.89) na biya kudin sadaki, Matashin da ya auri yar shekara 70

Taswirar jihar Borno
Ba a sace matafiya a Maiduguri ba: Rundunar soji ta bayyana abin da ya faru | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Daily Nigerian ta ruwaito Ado Isa na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“An jawo hankalin Operation Hadin Kai (OPHK) kan jerin rahotannin da ba su da tushe da ke yawo a kafafen sada zumunta a ranar 11 ga Disamba.
“Wasu jaridun kuma buga labarin sace matafiya zuwa Maiduguri da ‘yan kungiyar ISWAP suka yi a Mainok da Borgozo a karamar hukumar Kaga ta Borno."

Ya bayyana cewa, jita-jitar ba komai bane face karya, kuma ana kokarin bata kokarin rundunar ta soji ne.

Da yake bayyana gaskiyar abinda ya faru, Ado Isa ya ce:

“Gaskiyar lamarin shine ’yan kungiyar ta’addancin sun fito ne ta kauyukan Dole/Bari a cikin wasu motoci da nufin kafa shingen hanyoyi domin haifar da tashin hankali da fargaba a zukatan mazauna kauyuka da matafiya.
“Dakarun da ke sintiri a yankin gaba daya sun dakile yunkurin ba tare da bata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jirgin sama ya tarwatse da babban hafsan tsaron kasar Indiya

“Babu wani matafiyi da aka sace ranar Asabar. Hasashen masu yada barna ne da ba su ji dadin cewa sannu a hankali zaman lafiya ya dawo Arewa maso Gabas ba."

The Guardian ta rahoto cewa, Ado ya nanata kudurin rundunar na tabbatar da tsaro a kan titin mai cike da cunkoson jama’a tare da tabbatar da tsaro ga matafiya.

Ya kuma yi kira da aka kwantar da hankali tare da tabbatar da batutuwa daga rundunar sojoji kafin a yada a kafafen sada zumunta.

'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto

A jihar Sokoto kuwa, 'yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a a jam'i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rahoton ‘yan sanda: Dalibai biyu sun mutu, 12 sun jikkata a hatsarin babbar mota ranar Talata

Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai.

Dan majalisar jihar mai wakiltar mazabar Sabon Birni na Kudu, Sa'idu Ibrahim, ya tabbatar da harin, ya ce mutane ukun da suka jikkata suna karbar magani a babban asibitin Wamakko.

Ya ce wata mata, wacce aka harba a kauyen Dama, ta rasa kafar ta yayin da likitoci suka datse saboda an kasa gyara kafar.

Sojoji sun ceto 'yan sanda 20 da 'yan ISWAP da Boko Haram suka yi garkuwa dasu a Yobe

A wani labarin, hedkwatar tsaro ta sanar da cewa, an ceto 'yan sanda 20 da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a wani hari da suka kai wa sashen 'yan sanda da ke Buni Yadi a garin Buni Yadi.

Mukaddashin daraktan harkokin yada labarai na rundunar Birgediya Janar Benard Onyeuko, yayin da yake yiwa manema labarai karin haske kan ayyukan soji da ke gudana a cikin makwanni biyun da suka gabata ya bayyana hakan.

Kara karanta wannan

Za mu fatattaki APC daga madafun iko nan da 2023, Jerry Gana

Ya kuma ce sun fatattaki ‘yan ta’addan daga sansanoninsu yayin da wasa suka mika wuya, The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel