Jerin Mawaka 5 da suka fi kowa kudi a duniya
A yayin da kusan kowace shekara ake samun sauye-sauye, wani bincike da sanadin shafin yanar mujallar nan ta Forbes da ta gudanar a shekarar 2018, Legit.ng ta kawo muku jerin attajiran mawakan duniya biyar tare da hotunan su da adadin dukiya.
5. Aubrey Drake Graham
Wannan mawaki dan asalin kasar Canada mai shekaru 31 a duniya ya shahara da sunan Drake. Yana da tarin dukiya ta kimanin $100m.
4. Marshall Bruce Mathers III
Marshall ya shahara da sunan sa na fagen waka na Eminem kuma ya kasance haifaffen kasar Amurka. Ya na da shekaru 45 da tarin dukiya ta kimanin $100m.
3. Andre Romelle Young
Baya ga siffar karfin jiki, wannan mawaki yana kuma da zurfin aljihu mai tarin dukiya ta kimanin $770m. Ana yiwa wannan mawaki dan kasar Amurka lakabi da sunan Dr. Dre. Yana kuma da shekaru 53 a duniya.
2. Sean John Combs
Wannan haifaffen kasar Amurka mai shekaru 48 a duniya yana da tarin dukiya ta kimanin $825m. Ana masa lakabi da sunayen Puff Daddy, Puffy, P. Diddy, Diddy, Brother Love da kuma Love.
1. Shawn Corey Carter
Bayan kusan shekaru biyar da suka gabata wannan mawaki yana zuwa a mataki na biyu, wannan shekarar mawakin mai lakabin Jay -Z ya bude wuta inda yake da tarin dukiya ta kimanin $900m. An haifi Jay-Z ne a kasar Amurka kuma yana da shekaru 48 a duniya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng