NCC ta ankarar da jama’a, ‘yan damfaran Iran su na harin na'urori da wayoyin ‘Yan Najeriya

NCC ta ankarar da jama’a, ‘yan damfaran Iran su na harin na'urori da wayoyin ‘Yan Najeriya

  • Hukumar kula da sadarwa ta Najeriya tace masu kutse na kokarin damfarar mutane a Najeriya
  • A wata sanarwa da ta fito a yau, NCC ta ja-kunnen jama’a game da kamfanin Iran mai suna Lyceum
  • Lyceum suna yi wa mutane kutse, sun yi kaurin-suna a kasashe irinsu Saudiyya, Israila da sauransu

Abuja - Hukumar kula da sadarwa ta kasa watau NCC, tace an kawo mata karar wata kungiyar ‘yan kutsen yanar gizo a kasar Iran mai suna Lyceum.

Jaridar Punch ta rahoto hukumar NCC tana cewa kungiyar ta Lyceum tana harin kamfanonin sadarwa da masu bada damar ziyartar shafukan yanar gizo.

Masu kutsen na neman yadda za su kai hari ga ma’aikatar kasar wajen Najeriya da na kasashen Afrika.

Rahoton yace wannan kungiya da aka fi sani da Hexane, Siamesekitten ko Spirlin yana harin kamfanonin ne da nufin su kai masu hari ta yanar gizo.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun kai wani mummunan hari Kaduna, sun kashe mutane

Jaridar The Eagle ta fitar da jawabin da hukumar NCC tayi a ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba, 2021, tana fadakar da mutane a kan sharri kungiyar Lyceum.

NCC ta ankarar da jama’a, ‘yan damfaran Iran su na harin na'urori da wayoyin ‘Yan Najeriya
Ana damfarar mutane ta gafaka Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Nigerian Computer Emergency Response tace ayi hattara

"Bayani kan harin yanar gizon ya zo cikin shawarwarin da tawagar da ke daukar matakin gaggawa. The ngCERT yana ganin yiwuwar ta’adin yana da karfi.”
“Wannan kungiya sun yi suna wajen yi wa kamfanonin layin waya da ISPs kutse. Tsakanin Yuli da Oktoban 2021, an samu Lyceum da kai hari a kasashen Israila, Maroko, Tunisiya, da Saudi Arabiya.” - NCC.

Yadda Lyceum yake yi wa mutane ta’adi - NCC

“Da zarar Lyceum sun yi nasarar kutsawa na’urar mutum, za su rika bibiyar al'amuransa Daga nan sai su aikowa mutum tsutsotin Shark da Milan

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

NCC tace Lyceum da aka fi sani da yi wa kamfanonin gas na kasashen gabas ta tsakiya adawa, ya fara kai hari ga irin wadannan kamfanoni na sadarwa da ISP.

Idan ‘yan kutsen suka kai ga na’urorin mutane, sai su nemi kai hari ga shugabanni da manyan kamfanonin, don haka ake kira a sa ido wajen hawa yanar gizo.

COVID-19: Najeriya ta kashe N9.9 a kan goge hannuwa

Kwanakin baya ne majalisar FEC ta amince a kashe Naira tiriliyan 2.3 da nufin kare tattalin arzikin Najeriya daga annobar cutar COVID-19 da ta addabi Duniya.

Man goge hannu da shirye-shiryen matasa sun ci kusan N10bn domin yakar Coronavirus. Haka zalika an ba 'yan kasuwa biliyoyin kudi ta karkashin bankin CBN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel