ASUU: Malaman Jami’a za su hadu da Gwamnati a kan yiwuwar sake shiga yajin-aiki

ASUU: Malaman Jami’a za su hadu da Gwamnati a kan yiwuwar sake shiga yajin-aiki

  • Kungiyar ASUU za ta hadu da bangaren Gwamnatin Tarayya a makon nan
  • Ana sa ran a zaman za a san makomar ASUU kan sake shiga wani yajin-aiki
  • Malaman Jami’a suna zargin Gwamnatin Buhari da saba alkawuran da tayi

Abuja - Bayan tsawon makonni babu wata magana tsakanin gwamnatin tarayya da malaman jami’o’i, kungiyar ASUU tace za suyi wani zama a makon nan.

Bangarorin za su tattauna kan rashin cika alkawuran da gwamnatin tarayya ta dauka a lokacin da aka janye wani dogon yajin-aiki a Disamban shekarar 2020.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya kyankyasawa manema labarai wannan a lokacin da ya yi magana da jaridar Nigerian Tribune.

Da aka tuntubi shugaban na ASUU a makon da ya wuce, sai yace za su yi wani zama a makon nan.

Kara karanta wannan

Duka Gwamnonin jihohin Arewa 19 za su yi muhimmin taro a kan batun harajin VAT

Rahoton yace Farfesa Emmanuel Osodeke bai bayyana asalin ranar da za a yi zaman ba, amma ya tabbatar da cewa ASUU za ta hadu da wakilan gwamnatin kasar.

Kungiyar ASUU
Wakilan ASUU da 'Yan Majalisar Tarayya Hoto: africannewstoday.com
Asali: UGC

Emmanuel Osodeke yake cewa duka bangarorin biyu ne suka cin ma matsayar ayi wannan taro. Jaridar tace za a yi wannan zama a babban birnin tarayya, Abuja.

Jaridar Punch tace kungiyar malaman jami’an sun koka game da shirun da gwamnati tayi.

Kungiyar ASUU ta ba gwamnatin Muhammadu Buhari zuwa karshen watan Agusta, ta cika alkawuran da ta dauka, ko kuma a sake rufe jami’o’in gwamnati.

Ina alkawuran da aka yi wa ASUU a 2020?

Kusan wata guda da wuce war wannan wa’adi, har yanzu ba a dauki wani kwakkwaran mataki ba.

Yarjejeniyar da ASUU tayi da gwamnatin tarayya sun hada da fitar da kudi domin a gyara jami’o’i, ta yadda za a samu wuraren kwana da dakunan karatu masu kyau

Kara karanta wannan

FG ta gano kuma ta taka wa masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya birki, Malami

Sannan malaman jami’ar suna jiran gwamnatin Najeriya ta biya su alawus din karin aiki na EAA. Har ila yau, ASUU na so a rabu da manhajar IPPIS, a koma wa UTAS.

Asalin abin da ya faru - Minista

Idan za ku tuna, a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta, 2021, gwamnatin tarayya ta bayyana abin da ya sa ba ta iya cika alkawuran da tayi wa malaman jami’a a 2020 ba.

Karamin Ministan ilmi na kasa, Emeka Nwajiuba, ya bayyana cewa bankin CBN na kokarin tura kudin habaka jami’o’in. amma ASUU ba ta yarda da wannan bayani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng