Mai kudin duniya ya yi alkawarin bada kyautar $6bn idan akayi masa bayanin yadda za'a kashe

Mai kudin duniya ya yi alkawarin bada kyautar $6bn idan akayi masa bayanin yadda za'a kashe

  • An yi musayar kalamai tsakanin shugaban shirin kawar da yunwa na duniya da mutum mafi arziki a duniya
  • Attajirin ya yi alkawarin bada kyautar makudan biliyoyin kudi da sharadin a yi masa bayanin yadda za'a kashesu
  • Shirin WFP na taimakawa wajen samar da abinci ga jama'a marasa galihu a sansanin gudun hijra a fadin duniya

Landan - Mai kudin duniya, Elon Musk, ya kalubalanci majalisar dinkin duniya ta bayyana masa yadda $6bn zai magance yunwa a duniya kuma idan tayi kai tsaye zai bada kudin.

Jawabansa ya biyo bayan kalaman da Diraktan yaki da yunwa na duniya WFP, David Beasley, ya kalubalanci attajiran duniya musamman mutum biyu mafi kudi Jeff Bezos da Elon Musk su taimaka da kudi.

Kara karanta wannan

So makaho: Matashi ya fada soyayyar 'yar fim da ta girme shi, ya daina cin abinci saboda begenta

David Beasley ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da CNN makon da ya gabata.

Yace:

"$6 billion zai taimakawa mutum milyan 42 da ke gab da mutuwa idan ba'a taimaka musu ba."

A cewarsa wannan kashi 2% ne kadai cikin arzikin Elon Musk.

Shi kuma Elon Musk a nasa martanin ranar Lahadi a Tuwita, ya bayyana cewa:

"Idan WFP za tayi bayani a Tuwita yadda $6 billion zai magance yunwa a duniya. Zan sayar da hannun jari na a Tesla yanzun nan kuma in bada kudin."
"Amma wajibi ne ayi komai a fili, saboda jama'a su ga yadda za'a kashe kudin."

Mai kudin duniya ya yi alkawarin bada kyautar $6bn
Mai kudin duniya ya yi alkawarin bada kyautar $6bn idan akayi masa bayanin yadda za'a kashe Hoto: Elon Musk
Asali: Getty Images

Beasley kuwa yayi martanin cewa majalisar dinkin duniya na da shirye-shirye a kasa dake nuna yadda za'a kashe kudi ba rufa-rufa.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Dalilai 2 da suka sa EFCC ta yi ram da biloniya Obi Cubana

Yace:

"Za ka iya turo wakilanka su duba shirinmu domin samun tabbacin haka,".
"$6 billion ba zai magance yunwa a duniya ba, amma zai takaita gudun hijra, zai taimakawa mutum milyan 42 dake cikin halin yunwa."

Kawo ranar Litinin, arzikin Elon Musk ya kai $311 billion, bisa binciken Bloomberg Billionaire Index, kuma shine mutum mafi arziki a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel