Dalla-dalla: Dalilai 2 da suka sa EFCC ta yi ram da biloniya Obi Cubana

Dalla-dalla: Dalilai 2 da suka sa EFCC ta yi ram da biloniya Obi Cubana

  • A daren Litinin ne labaran cafke biloniya Obi Cubana ya karade kafafen sada zumunta
  • EFCC ta bayyana cewa ta kama shi ne kan zargin halatta kudin haram da zambar haraji
  • Obi Cubana ya yi suna a Najeriya ne tun bayan kudin da ya zubar yayin birne mahaifiyarsa

Ba sabon labari ba ne cewa Obinna Iyiegbu, wanda aka fi sani da Obi Cubana ya na hannun hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC a Abuja.

Legit.ng ta tattaro muku cewa, hukumar yaki da rashawan ta gayyacesa ne kan dalilai guda biyu kwarara.

Dalla-dalla: Dalilai 2 da suka sa EFCC ta yi ram da biloniya Obi Cubana
Dalla-dalla: Dalilai 2 da suka sa EFCC ta yi ram da biloniya Obi Cubana. Hoto daga @obi_cubana
Asali: Instagram

Domin bayani ga makaranta, Legit.ng ta bayyana dalilai biyu da yasa Obi Cubana ya ke hannun EFCC domin amsa tambayoyi.

Ga dalilan kamar haka:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Halatta kudin haram

Wannan babban laifi ne daga cikin laifuka a kasar nan. Wata hanya ce da ake bi wurin adana kudi mai yawa da aka samo wurin aikata laifuka kamar safarar miyagun kwayoyi ko kuma ta'addanci.

Sai a mayar da kudin tamkar na halas ko kuma an samo su daga halastacciyar hanya. Wadannan kudaden kuma kazantattu ne kuma boye su da aka yi tare da bayyana su a matsayin na halas laifi ne.

2. Zambar haraji

Zambar haraji wani nau'in laifi ce daga manyan laifuka. Ta na faruwa ne idan mutum ko kasuwancinsa da gangan tare da son rai ya bada bayanan karya kan yawan harajinsu.

Ana kuma iya bayyana shi a matsayin hanya da wasu mutane ke bi ta kin biyan haraji gaba daya.

Bayan kama shi da aka yi, 'yan Najeriya sun yi martani daban-daban. Wasu sun kushe kamen yayin da wasu ke cewa tabbas ya fuskanci shari'a idan an kama shi da laifi.

EFCC ta cafke yaro da mahaifiyarsa wacce ya tsoma a harkar damfara ta yanar gizo

A wani labari na daban, hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) a shiyyar Kaduna ta cafke wasu mutane hudu da suka hada da Lucky Ebhogie, Richman Kas Godwin, Israel Justin da Precious Iwuji da aikata laifin zambar ta yanar gizo.

An damke su ne a ranar 5 ga Agusta, 2021, a unguwar Sabo da ke Kaduna, a Jihar Kaduna biyo bayan bayanan sirri kan zarginsu da hannu a ayyukan damfara ta yanar gizo, Daily Nigerian ta ruwaito.

Bincike ya nuna cewa wadanda ake zargin galibi suna da hannu cikin aikata zamba da kulla soyayyar karya soyayya; yin karya da sunan ma'aikatan sojin Amurka akan ayyukan kasashen waje don yaudarar mutanen da suka fada fatsarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel