Da duminsa: Osinbajo da Tinubu sun hadu ana tsaka da rade-radin baraka a tsakaninsu

Da duminsa: Osinbajo da Tinubu sun hadu ana tsaka da rade-radin baraka a tsakaninsu

  • Ana tsaka da rade-radin barakar da ke tsakanin Tinubu da Osinbajo, sun ci karo a garin Abuja a ranar Juma'a
  • Dukkan 'yan siyasan biyu sun bayyana farin cikin haduwa da juna inda cike da walwala suka rungume juna
  • Kamar yadda ake yadawa, Osinbajo na hararo gadar kujerar Buhari yayin da jagaban Tinubu ya ke hango hakan

Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da Asiwaju Bola Tinubu, jigon kuma uban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun hadu a Abuja a ranar Juma'a.

Daily Trust ta ruwaito cewa, sun rungume juna cike da farin ciki yayin da ake ta rade-radin su biyun ba su ga maciji saboda kowa na son fitowa takarar shugabancin kasa a 2023.

Daga Tinubu har Osinbajo, babu wanda ya fito fili ya bayyana bukatarsa na son fitowa takarar, amma akwai alamun cewa dukkansu suna son maye gurbin Buhari.

Kara karanta wannan

2023: Fitattun 'yan siyasan Najeriya 11 da suka ce sai Tinubu

Da duminsa: Osinbajo da Tinubu sun hadu ana tsaka da rade-radin baraka a tsakaninsu
Da duminsa: Osinbajo da Tinubu sun hadu ana tsaka da rade-radin baraka a tsakaninsu. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel