Nan da shekaru 49 arzikin man Najeriya zai kare, Bankin Duniya

Nan da shekaru 49 arzikin man Najeriya zai kare, Bankin Duniya

  • Bankin Duniya ta yi kira ga wasu kasashe su fara tattalin arzikinsu saboda arzikin man feturinsu ya kara bushewa
  • Najeriya na cikin kasashen da aka lissafo rijiyoyin mansu zasu bushe muddin ba'a samo wasu ba nan da shekaru 50
  • Bankin yace wadannan kasashe na kashe kudaden da suke samu yanzu kan abubuwan da basu dace ba maimakon tattali

Bankin duniya ya bayyana cewa arzikin man feturin kasashe irinsu Najeriya, Ecuador da Chile na da kasa da shekaru 50 kafin ya kare gaba daya.

Shiyasa bankin ke baiwa wadannan kasashe shawara su fara neman wasu hanyoyin zuba jari da samun kudi irinsu sashen Ilmi, cigaban zamani kafin lokaci ya kure.

Wannan na kunshe cikin rahoton da Bankin duniyan ta saki ranar Laraba, 27 ga Oktoba, 2021, mai taken "Canzawar arzikin kasashe 2021.".

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya zata karbi bashin N290bn don samarwa yan Najeriya ruwan sha

A rahoton da Leadership ta tattaro, muddin ba'a samu wasu sabbin rijiyoyin man fetur ba a Najeriya, toh wadanda ake hakar mai zasu bushe nan da shekaru 49 amma dai arzikin Gas zai rage.

Rahoton ya kara bayani kan wasu kasashe 18 da arzikin man feturinsu zai kai shekaru sama da 200 kafin ya kare.

Yace:

"Kasashe masu arzikin mai irinsu Najeriya da Ecuador ka iya karar da arzikin man feturinsu nan da shekaru 50 dubi ga yadda suka diba yanzu, muddin ba'a samu wasu sabbin rijiyoyin mai ba."
"Kasashe masu arziki irin wannan basu yi amfani da kudaden da suke samu ta hanyar da ya dace ba."
"Idan aka cigaba da kashe kudaden haka, zai shafi arzikin wadannan kasashe ranar gobe."

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun ceci mutumin da ya hau hatsumiya yana kokarin kashe kansa a Legas

Saura shekaru 49 arzikin man Najeriya ya kare
Nan da shekaru 49 arzikin man Najeriya zai kare, Bankin Duniya Hoto: NNPC

Gwamnatoci su samawa kansu mafita

Bankin ya cigaba da cewa maimakon zuba jari da abubuwan kwarai da kudaden da ake samu ta man feturin da ake haka yanzu wajen inganta rayukan al'umma, cin kudaden kawai ake yi.

An baiwa kasashe shawara su samar da dokokin da shirya-shiryen samar da wasu hanyoyin samun kudi da ka iya maye gurbin arzikin man fetur.

Rahoton yace:

"Dalilin haka shine ana kashe arzikin da ake samu ta wannan dukiya (mai) mai makon zuba jari da su wajen inganta mutane ko gine-ginen kayan alfanu."
"Saboda haka ana bada shawara gwamnatoci su samar da dokokin tattalin wannan arziki da azurta mutane ko su samar da wasu sabbin hanyoyin samar da kudi."

Asali: Legit.ng

Online view pixel