Majalisar dattawa tayi Alla-wadai da shirin karban bashin N290bn don samar da ruwan sha

Majalisar dattawa tayi Alla-wadai da shirin karban bashin N290bn don samar da ruwan sha

  • Mambobin Majalisar dattawa sun yi Alla-wadai da shirin karban bashin $700 million da gwamnatin tarayya ke shirin yi
  • Gwamnati zata karbawa ma'aikatar ruwa bashin ne a 2022 don samawa yan Najeriya isasshen ruwan sha
  • Daya daga cikin Sanatocin yace sam ba dashi za'a yi haka ba, rainin hankalin ya isa haka

Abuja - Kwamitin Mambobin majalisar dattawa kan basussukan gida da waje sun yi watsi da bukatar Shugaba Muhammadu Buhari na karbar bashin $700 million (N290bn) don ma'aikatar ruwa.

Ma'aikatar ruwan za tayi amfani da kudin ne wajen samar da isasshen ruwan sha ga yan Najeriya a karkara da birane karkashin shirin SURWASH.

Mambobin kwamitin majalisar sun bayyana rashin yardarsu da wannan bashi da gwamnatin ke shirin karba, rahoton ThisDay.

Sun bayyana hakan yayinda manyan jami'an ma'aikatar suka gurfana gabansu domin bayani kan abinda suke niyyar yi da kudaden da suka bukata cikin kasafin kudin 2022 da Buhari ya gabatar kwanaki.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya zata karbi bashin N290bn don samarwa yan Najeriya ruwan sha

Gwamnatin tarayya zata karbi bashin N290bn don samarwa yan Najeriya ruwan sha
Gwamnatin tarayya zata karbi bashin N290bn don samarwa yan Najeriya ruwan sha
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da farko, Shugaban kwamitin, Sanata Clifford Ordia, yace sau uku kenan da ake baiwa ma'aikatar damar karban bashi, saboda haka suyi bayani kan abubuwan da sukayi da kudade.

Yace:

"An baiwa ma'aikatar ruwa damar karban bashin $450 million daga wajen bankin cigaban Afrika AfDB, sannan kuma $6 million daga bakin AfDB kuma don aikin ruwan Gurara."
"Kuyi mana bayanin abinda za kuyi da $700 million don ayyukan ruwa."

Saboda haka kwamitin ta ce an gayyaci Ministan arzikin ruwa, Adamu Suleiman, ya bayyana gabanta don bayani kan basussukan da aka karba a baya da kuma wadanda ake son karba, a riwayar Thisday.

Ba da ni za'ayi haka ba

Bayan haka, Sanata Obinna Igba yace sam ba za'a yi haka da shi ba, ba zai amince a karbi wannan bashi ba.

Kara karanta wannan

Hush-Kyari: Saura kiris duniya ta san makomar Abba Kyari, FDC zai ba da rahoto

A cewarsa:

"Wannan bashi ba da ni ba, gaskiya rainin hankalin ya isa haka."

Sakatariyar din-din-din na ma'aikatar ruwa, Mrs Esther Did Walson-Jack ta gaza bayani gamsasshe kan basussukan da suka karba a baya.

Kasafin kudin 2022: Ma'aikatar Lafiya na shirin karban bashin N82bn don sayen ragar kariya daga cizon sauro

Majalisar dattawar Najeriya ta yi Alla-wadai da shirin da ma'aikatar kiwon lafiyan Najeriya ke yi na karban bashin $200 million (N82,070,388,916.76) a kasafin kudin shekarar 2022.

Sakaraten din-din-din na ma'aikatar ya bayyanawa kwamitin a taron bayani kan kudin da ma'aikatar ta bukata cikin kasafin kudin 2022.

Daya daga cikin mambobin kwamitin kiwon lafiya na majalisar dattawa, Gershom Bassey, ranar Talata ya ce sam ba dashi za'a yi wannan ba.

Bassey ya laburtawa Sakaraten din-din-din na ma'aikatar cewa wannan kudi na bilyan 82 da ake shirin karba bashi don sayan ragar Malariya yayi yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel