Babban magana: Gwamnatin Kano ta rufe wani asibitin kudi saboda wasu mace-mace

Babban magana: Gwamnatin Kano ta rufe wani asibitin kudi saboda wasu mace-mace

  • Hukumar kula da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu ta jihar Kano ta rufe wani asibitin kudi a jihar saboda wasu mace-mace biyu da aka samu a asibitin cikin watanni shida
  • Hukumar ta dauki matakin ne biyo bayan rahoton da ta samu daga wani kwamitin jama’a kan mutuwar wasu majinyata biyu a cibiyar lafiyar
  • An gano cewa likitan fida na asibitin shi kadai ke gudanar da ayyukan da ya kamata ma'aikatan jinya hudu su gudanar

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta rufe wani asibitin kudi a jihar saboda wasu mace-mace biyu da aka samu a asibitin cikin watanni shida.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, Hukumar kula da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu (PHIMA) ce ta rufe asibitin mai suna, Green-Olives Hospital, wanda ke Sabon Titi, Tal’udu Gadon Kaya a karamar hukumar Gwale.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun saki ‘yan asalin jihar Benue da suka sace a Zamfara

Babban magana: Gwamnatin Kano ta rufe wani asibitin kudi saboda wasu mace-mace
Babban magana: Gwamnatin Kano ta rufe wani asibitin kudi saboda wasu mace-mace Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

An tattaro cewa matakin hukumar ya biyo bayan rahoton da ta samu daga wani kwamitin jama’a kan mutuwar wasu majinyata biyu a cibiyar lafiyar.

Babban Sakataren PHIMA, Dr Usman Tijjani Aliyu, wanda ya sanar da rufe cibiyar lafiyan a wata sanarwa, ya ce hukumar ta binciki lamarin sosai inda ta gano cewa akwai rashin bin ka'ida da kuma rashin gudanar da ayyukan da ake yi wa marasa lafiya yadda ya kamata a cibiyar.

Sanarwar ta ce:

Likitan da ke tiyata shine ke aiki a matsayin ma'aikacin jinya mai sa bacci, ma'aikacin jinya mai taimakawa a dakin tiyata da kuma mataimakin likitan fida, don haka shi kadai yake yin ayyuka hudu yayin tiyata, kuma wannan rashin bin ka'ida ne ga kowane bangare.

"Haka kuma ba a sanya hannu kan fam din izini kafin tiyata, marasa lafiya ba sa shiri yadda ya kamata kafin tiyata sannan kuma ba a sanya ido kan marasa lafiya a lokacin tiyata."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta amince da biyan kudin kammala titin Gombe zuwa Biu

Dr Adamu ya roki mazauna da su kai rahoton irin wadannan lamura a ko'ina a Kano don daukar matakin gaggawa.

Ya kuma ba da tabbacin cewa za a hukunta mai laifin kamar yadda hukumar ta tanada, ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da hada kai da jama’ar jihar Kano da sauran kungiyoyin farar hula domin yakar rashin da'a a bangaren lafiya, rahoton Solace base.

Gwamnatin Kano za ta shuka itatuwa guda miliyan ɗaya a fadin jihar

A wani labarin, gwamnatin jihar Kano ta ce ta ƙaddamar da shirin shuka itatuwa miliyan daya a kananan hukumomi 44 na jihar don dakile illar ɗumamamar yanayi da sare itatuwa, The Guardian ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma ce ta rattaba hannu kan yarjejeniya da wani kamfanin tsaftace muhalli na shekara 20 don tsaftace gari da samar da makamashi daga shara/bola.

Kwamishinan muhalli na jihar, Dr Kabiru Getso, wanda ya kaddamar da shirin ya ce gwamnatin za ta fara shirin shuka itatuwan da hadin gwiwar Givfree Africa kafin damina ta wuce a cewar rahoton na The Guardian.

Kara karanta wannan

Buhari ya kashe sama da N45bn domin inganta rayuwar Katsinawa, Masari

Asali: Legit.ng

Online view pixel