Gwamnatin Kano za ta shuka itatuwa guda miliyan ɗaya a fadin jihar

Gwamnatin Kano za ta shuka itatuwa guda miliyan ɗaya a fadin jihar

  • Gwamnatin jihar Kano za ta shuka itatuwa guda miliyan ɗaya a kananan hukumomi 44 na jihar
  • Gwamnatin ta ce za a shuka itatuwan ne domin yaki da dumamar yanayi, kwararowar hamada da wasu matsalolin muhalli
  • Dr Kabiru Getso, Kwamishinan muhalli na jihar Kano ne ya sanar da hakan yana mai cewa shirin zai taimaka inganta lafiya

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ce ta ƙaddamar da shirin shuka itatuwa miliyan daya a kananan hukumomi 44 na jihar don dakile illar ɗumamamar yanayi da sare itatuwa, The Guardian ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma ce ta rattaba hannu kan yarjejeniya da wani kamfanin tsaftace muhalli na shekara 20 don tsaftace gari da samar da makamashi daga shara/bola.

Gwamnatin Kano za ta shuka itatuwa guda miliyan ɗaya a fadin jihar
Shuka itatuwa. Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Kwamishinan muhalli na jihar, Dr Kabiru Getso, wanda ya kaddamar da shirin ya ce gwamnatin za ta fara shirin shuka itatuwan da hadin gwiwar Givfree Africa kafin damina ta wuce a cewar rahoton na The Guardian.

Dr Getso ya ce an dauki matakin ne biyo bayan tsare-tsaren gwamnati da ake yi kan kare muhalli, dakile ambaliyar ruwa, kwararowa hamada da sauransu.

Mummunan zafin da aka yi bara a Kano na da nasaba da rashin itatuwa, Dr Getso

Getso ya ce tsananin zafin da aka yi a Kano a bara yana da nasaba da tashin shuka itatuwa. Ya bukaci masu ruwa da tsaki su jajirce don ganin an cimma burin da aka saka a gaba.

Kwamishinan ya bukaci mazauna Kano su rika tsaftace muhallinsu, su guji bahaya a fili su kuma tabbatar suna amfani da ruwa mai tsafta don kiyaye bullar cutar kwalara.

Getso ya kara da cewa:

"Gwamnati ta tanada tsare-tsare don magance ƙallubalen muhalli da ke adabar jihar. Mun kafa hukumar shuka itatuwa na Kano, don ta riƙa kula da shuka itatuwa. Mun kuma shiga tsarin National Green Wall Project na kasa inda aka samar da fili don shuka itatuwa a unguwanni."

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da sabbin kalolin fentin ababen hawa na haya a fadin jihar

Ya cigaba da cewa gwamnati ta kuma samar da N500m da filin gina ofishin hukumar kiyaye kwararowar hamada ta NEWMAP tare da hadin gwiwa da ofishin asusun kula da muhalli na ƙasa don kafa cibiyar sarrafa shara/bola a Challawa, Sharada da Bompai.

Gwamnatin ta kuma yi dokoki don tabbatar da cewa al'umma sun bi dokokin tare da ɗaukan jami'an duba gari 1000 da za su sa ido don ganin an bi dokokin.

2023: Ba mu buƙatar Atiku ya sake takara, Ya tafi Dubai ya manta da mu tunda ya sha kaye a 2019, Ƙungiyar PDP

A wani labarin daban, wata kungiya mai suna People’s Democratic Party (PDP) Action 2023, ta bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kada ya sake takara a shekarar 2023 don ya yi watsi da jam'iyyar ya koma Dubai, UAE, tunda ya fadi zabe a 2019, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kisan Jos: Na kudiri aniyar gurfanar da 'yan ta'adda a gaban kuliya, inji Buhari

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, bai riga ya bayyana niyarsa na son sake takara ba a 2023, amma, dansa, Adamu Atiku Abubakar, ya tabbatar cewa zai sake takara.

Amma a martaninsa, Atikun ya ce ba watsi da jam'iyyar ta PDP ya yi ba, ya tafi yin karatun digiri na biyu ne a kasar waje.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel