Ku faɗa mana masu ɗaukan nauyin 'yan ta'adda: Ƙungiyar musulmi ta ƙallubalanci gwamnatin Buhari

Ku faɗa mana masu ɗaukan nauyin 'yan ta'adda: Ƙungiyar musulmi ta ƙallubalanci gwamnatin Buhari

  • Kungiyar musulmi ta Ansar-Ud-Deen ta yi kira ga gwamnatin Buhari ta tona asirin wadanda ke daukan nauyin 'yan ta'adda
  • Alhaji Isiaq Sanni, sakataren kungiyar ne ya yi wannan kirar yayin taron da aka yi bayan rasuwar tsohon shugaban kungiyar Alhaji Liadi Adeyinka
  • Sanni ya bayyana marigayi Liadi Adeyinka a matsayin mutum wanda ya dage wurin ilmantar da al'umma don ya yi imanin hakan zai magance rashin tsaro

Kaduna - Kungiyar musulunci ta Ansar-Ud-Deen yankin Arewa ta bukaci gwamnatin Nigeria ta tona asirin masu daukan nauyin 'yan bindiga da 'yan ta'adda a kasar, rahoton SaharaReporters.

Sakataren kungiyar musulmin, Alhaji Isiaq Sanni ne ya yi wannan kirar a garin Kaduna yayin da ya ke waiwaye kan rayuwar tsohon shugaban kungiyar, marigayi Alhaji Liadi Adeyinka wanda ya rasu a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari

Ku fada mana masu ɗaukan nauyin ta'addanci: Kungiyar musulunci ta ƙallubalanci gwamnatin Buhari
Kungiyar musulunci ta ƙallubalanci gwamnatin Buhari bayyana sunan masu daukan nauyin 'yan ta'adda. Hoto: SaharaReporters
Asali: Facebook

Sanni ya ce marigayi Olapade ya yi aiki tukuru domin ganin mutane da dama sun samu ilimi, don yana ganin hakan wani hanya ce ta dakile rashin tsaro.

Ya kara da cewa abin kunya ne ganin yadda rashin tsaro ya yi katutu a kasar.

Ya ce:

"Abin takaici ne rashin tsaron da Olapade ya yi yaki da shi har yanzu bai kau ba. Don haka, muna kira da gwamnati ta kara kaimi wurin yakar yan bindiga da sauran kallubalen tsaro saboda abinda suke yi a yanzu bai magance matsalar ba.
"Gwamnati ta fada mana wadanda ke daukan nauyin yan bindiga, wadanda ke daukan nauyin rashin tsaro, domin mu san su wanene ba su son kasarmu ta cigaba, wadanda ba su son gwamnati."

Kara karanta wannan

Sarkin Birnin Gwari ya ce a yanzu 'yan fashi abinci suke nema maimakon kudin fansa

Yunwa ya saka 'yan bindiga a gaba, sun nemi a basu dafaffen abinci a matsayin kudin fansa

A wani labarin, kun ji cewa Ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna sun fara tambayar dafaffen abinci a matsayin kuɗin fansa, rahoton Daily Trust.

Ƴan bindigan sun janye kai hare-hare a garuruwa tun bayan da gwamnatin jihar ta soke cin kasuwannin mako-mako don daƙile rashin tsaro.

Wani shugaban matasa a ɗaya daga cikin ƙauyukan Birnin Gwari, Babangida Yaro ya shaidawa Daily Trust cewa tun bayan hana cin kasuwanni ƴan bindiga da ke sace mutane a ƙauyukan Kutemashi da Kuyello dafaffen abinci suke tambaya duk lokacin da suka sace mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel