An gano wata makabarta da ake binne layu a Kano

An gano wata makabarta da ake binne layu a Kano

- An gano wasu kaburbura a Kano inda ke binne wadansu layu da sauran abubuwa da ake kyautata zaton na tsafi ne

- Masu aiki a makabartar sun bayyana cewa sukan gano irin wadannan kaburburan ne saboda kwari da ke taruwa a wurin

- Ma'aikatan sunyi kira da gwamnati ta taimaka ta sanya musu fitilu da za su rika haska makabartar da dadare

An gano wata makabarta da ake binne layu a Kano
An gano wata makabarta da ake binne layu a Kano
Asali: Twitter

Ma'aikatan da ke kulawa da makabarta a jihar Kano sun gano wadansu layu da aka binne a kaburbura a wata makabarta da ke jihar.

Daya daga cikin ma'aikatan wanda ya kai kimanin shekaru 13 yana aikin hakar kabari a makabartar Tukuntawa mai suna Abu Gwadabe ya fadawa Bbc yadda suke gano layun da ake binne wa a makabartar.

DUBA WANNAN: An kashe kuku bisa zarginsa da sata a gidan gwamna Dankwambo

Ya ce, "Galibin layun da sauran abubuwan da ake binne wa a kaburburan suna dauke da wani turare wanda dabobi kamar kunama da kwari ke son qamshinsa. Hakan yasa idan muka iso makabartar da safe muka lura kwari ko kuda sun taru a wani waje, sai mu haqa wurin."

Wani ma'aikacin makabartar da ya shafe shekaru 11 yana aiki a makabartar, Uba Ibrahim ya mika rokonsa ga gwamnati da ta samar da fitilun lantarki da za su taimaka wajen aikata irin wadannan miyagun ayyukan a makabartar.

Al'umma da damu suna alaqanta irin wannan binne-binnen da ake yi a makabartu da tsibu ko tsafi domin samun wasu bukatu na duniya.

Ana samun qaruwar afkuwar irin wadannan ayyukan ne lokutan da zabuka suke qaratowa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: