Yadda za a rage radadin ciwon sikila a jikin masu cutar

Yadda za a rage radadin ciwon sikila a jikin masu cutar

A yau ne ake bikin Ranar sikila ta Duniya. Wannan ya sa mu ka kawo wasu dabaru da Masana kiwon lafiya su ka gindaya domin ganin masu wannan cuta mai matukar illa sun rage fama da rashin lafiya.

Manyan hanyoyin da za a bi wajen ganin wannan cuta ta sikila ta lafa sun hada da:

1. Shan magani kullum

A kullum, a na so mai dauke da wannan cuta ya rika shan magunguna irin su Folic acid da sauran sinadarorin da ke gina kwayoyin jinin jiki. Likitoci kan rubuta irin magangunan da za a rika sha.

2. Cin kayan marmari

A na so mai dauke da wannan cuta ya lakanci ci da shan kayan marmari da kuma sauran kayan abinci da ke dauke da sinadaran bitamin. A na kuma so maras lafiya ya rika cin ganye da hatsi.

3. Gujewa yanayi mai tsanani

Masana sun ce mai dauke cutar sikila ya guji zama a wuraren da ke da matsanancin zafi ko kuma matukar sanyi. Irin wannan yanayi ya kan farfadowa marasa lafiya da wannan muguwar cuta.

KU KARANTA: Adadin Mutanen da a ka hallaka a mulkin Buhari

4. Atisaye

Likitoci sun bayyana cewa motsa-jiki ya kan taimaka wajen hana cutar sikila tashi. Sai dai kuma ba a so masu wannan cuta su yi ta faman atisaye har ya wuce gona da iri, hakan ya na da illa.

5. Ruwa

Babbar hanyar da za a bi wajen hana cutar sikila tashi shi ne shan ruwa. A na so masu dauke da cutar ta sikila su yi ta kwalkwalar ruwa sosai da gaske. Bushewar jiki ya na illa ga mai sikila.

Daga cikin sauran hanyoyin da ake bi wajen maganin wannan cuta a duk lokacin da ta tashi akwai; karin jini, da kuma canjin bargon kashi da ake yi wa musamman kananan yara masu karancin shekaru.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng