'Zan Mutu Ranar Lahadi," Fitaccen Malamin Addini a Najeriya Ya Hango Ajalinsa

'Zan Mutu Ranar Lahadi," Fitaccen Malamin Addini a Najeriya Ya Hango Ajalinsa

  • Pastor Enoch Adeboye ya bayyana cewa ya hango cewa zai mutu a wata ranar Lahadi bayan ya gama ibada, kuma ya ci sakwara
  • Shugaban cocin na RCCG ya ce zai mutu ba tare da wata rashin lafiya ba, don a cewarsa, ciwo ba shi ne alamar mutuwa ba
  • Ya shawarci Kiristoci su dage wajen neman bukatunsu a wajen Almasihu, ya kuma yi magana kan yin rayuwa a cikin talauci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Shugaban cocin RCCG, Pastor Enoch Adejare Adeboye, ya sake yin magana kan lokacin da ya ke ji a jikinsa zai bar wannan duniyar.

Malamin addinin Kiristan ya ce ya hango cewa zai mutu ne a wata ranar Lahadi, bayan ya gama halartar taron ibada, kuma ya ci sakwara.

Shugaban cocin RCCG, Pastor Enoch Adeboye ya ce zai mutu ranar wata Lahadi
Babban malamin Kirista kuma shugaban cocin RCCG, Pasto Enoch Adejare Adeboye. Hoto: @PastorEAAdeboye
Source: Facebook

Shugaban coci ya hango ranar da zai mutu

Kara karanta wannan

Ana batun yunwa, gwamnatin Tinubu ta fitar da ton 42,000 na hatsi a raba wa jihohi

Shugaban cocin na RCCG ya bayyana hakan ne a rana ta hudu na taron cocin na kasa da ke gudana kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin taron, Pastor Adeboye ya jaddada cewa ba kullum ne mutuwa take riskar marasa lafiya ba, yana mai nuni da cewa ko a shekaru biyu baya, ta taba magana a kan hakan.

Yayin da ya hakikance cewa zai yi mutuwar ba-zata, malamin cocin ya ce:

"Zan mutu ranar Lahadi bayan na gama ibada, na ci abincin da na fi so, watau sakwara, kuma zan mutu ne ba tare da wata rashin lafiya ba."

"Ku kare martabar ku" - Adeboye ga Kiristoci

Yayin da yake wa’azi mai taken “Ka hakura da abin da Ubangiji ya ba ka,” babban malamin addinin ya shawarci mabiyansa su dage wajen neman abubuwan bukatunsu a wajen Almasihu.

Kan batun wadata, Pastor Adeboye ya bayyana cewa:

“Wanda yake mallakar duniya da cikinta, kuma yake da azurfa da zinariya duka, ya biya tsananin farashi domin kada ku zama matalauta. Muddin kuna son ci gaba da zama talakawa, za ku kasance talakawa."

Kara karanta wannan

Dara ta ci gida: Yadda dan sanda ya tsere da gudu bayan kama kwamishinansu

Ya kuma tabo batun suka da ake yi wa Kiristocin da suka samu arziki, yana mai cewa:

“Idan ka samu nasara da arziki a matsayinka na Kirista, sai su fara zarginka. Idan ka mutu talaka, sai su rika tambaya, ‘Ina Allahn ka?’”
Malamin addinin Kirista, Enoch Adeboye ya ce akwai bukatar mutane su dage da addu'a don neman haihuwa
Babban malamin Kirista kuma shugaban cocin RCCG, Pasto Enoch Adejare Adeboye. Hoto: @PastorEAAdeboye
Source: Twitter

Shawarar Adeboye kan rashin haihuwa

Kan batun tsawon rai, jaridar Vanguard ta rahoto Pastor Adeboye na cewa:

“Tsawon rai naku ne. Amma shaidan yana son ya kashe ku da duk wata dabara da yake da ita. Dole ne ku tashi ku yaƙi shaidan don ceton rayuwarku.”

Ya kuma jaddada umarnin Ubangiji na haihuwa, yana kawo misalin mutanen littafin Injila irin su Rahila da Hana, waɗanda suka ci nasarar shawo kan rashin haihuwa ta hanyar addu’a.

- Pastor Enoch Adejare Adeboye.

Matasa sun farmaki cocin RCCG

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu fusatattun matasa sun farmaki cocin RCCG ta Pasto Enoch Adeboye ana tsakiyar gudanar da taron ibada.

Matasan da suka farmaki cocin da suka hada da maza da mata, sun lalata kayayyaki irinsu kujeru da gangunan cocin kamar yadda aka gani a bidiyo.

An ce shugaban cocin ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya tsayar da su daga abin da suke aikatawa, sai dai dole ya haƙura daga ƙarshe ya sanyawa sarautar Allah ido.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com