Babu wata kalma mai kama da Kirsimeti a littafin Injila – Babban Fasto
- Dr Daniel Olukoya, Shugaban cocin Mountain of Fire and Miracles Ministries ya ce cocin ba ta bikin Kirsimeti
- A cewar Fasto Olukoya, ba sa bikin ne saboda babu inda ke dauke da kalmar Kirsimeti a littafin Injila
- Ya gargadi Kiristocin zamani da su daina bunkasa wannan biki da ya saba ma koyarwar Injila
Shugaban cocin Mountain of Fire and Miracles Ministries, Dr Daniel Olukoya, ya ce cocin ba ta bikin Kirsimeti saboda hakan baya cikin littafin Injila.
Olukoya ya bayyana hakan a ne a ranar Laraba, 25 ga watan Disamba a lokacin wani shirin cocin wanda ya hade da bikin Kirsimeti na 2019, a hedkwatar cocin a ke Lagas.
Ya ce babu wani shafi a littafin Injila da ke dauke da Kalmar Kirsimeti ko cewar an haifi Yesu a ranar 25 ga watan isamba.
“Idan har ka karanci littafin Injila filla-filla, babu wata kalma mai kama da Kirsimeti.
“Kawai dai Injila na dauke da cewar makiyaya na kula da tumakansu a lokaci na sanyi sosai lokacin da suka hango tauraron da ya sanar da haihuwar Yesu Almasihu.
“Wannan lokaci na sanyi na iya kasancewa tsakanin Afrilu ko Mayu,” inji Olukoya.
A cewarsa, ranar 25 ga watan Disamba ya kasance wanda tsoffin Romawa suka ware domin bikin duniyar Mars ga masu bautar rana.
KU KARANTA KUMA: Zan yi bajinta fiye da na gwamnatin baya – Gwamnan Bauchi
Olukoya yace an hada haihuwar Almasihu da na bikin Mars ne domin samun shahara sannan aka sauya mata suna zuwa ‘Kirsimeti’.
Ya gargadi Kiristocin zamani da su daina bunkasa wannan biki da ya saba ma koyarwar Injila.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng